Marigayi Mahmoon Baba-Ahmed
Muhammad Bin Ibrahim
An fi saninsa a duniyar jarida a matsayin zaqaqurin d’an rahoto, musamman a zamanin siyasar jamhuriya ta biyu. Sunansa ya yi sharafi sosai a rahoton rikicin Mai-tatsine na Kano wanda Gidan Rediyon Tarayya Kaduna (FRCN) ya riqa yad’awa a farkon shekarun tamaninoni.
Bai yi zaman lumana da gwamnan Kano na lokacin ba, Alhaji Abubakar Rimi. Saboda galibin rahotanninsa suka ne ga ‘bangaren tsantsi na jam’iyyar PRP. Hakan ya kusantar da shi ga Sabo Bakin Zuwo. ‘Yan ‘bangaren ta’bo sun rungume shi ainun, musamman bayan sun kafa gwamnati a shekarar 1983.
A duniyar Adabi, marigayin ya rubuta waqoqi masu yawa da labarai cikin waqoqi. Kazalika ya fassara litattafan Williams Shakespare irin su Julius Cesar, Macbeth da Romeo and Juliet. Babban abin mamaki game da wannan fassara ta marigayin shi ne yadda ya yi ta cikin ainihin zubinta na baitocin waqe da sahihin harshe mai dad’in ji.
Daga baya ya kafa kamfanin Garkuwa Publications Limited wanda ya riqa wallafa jaridar SAWABA wacce ta yi wasu shekaru ana bugawa.
A shekarar 2004, na kasance muqaddashin edita na wannan jarida. Daga baya bayan jaridar ta tsaya, sai Sam Nda Isaiah, mawallafin jaridar LEADERSHIP ya fara wallafa jaridar Hausa mai suna LEADERSHIP HAUSA, ya kuma tuntu’bi marigayi da ya yi masa edita. Marigayin ya ce a’a, amma zai yi masa aikin tuntu’ba (consultancy) kuma zai ba shi matashin da zai masa aikin na edita. A ranar farko ta zuwa Abuja aikin wannan tuntu’ba, ni ne marigayi ya d’auka don taya shi.
A iya zaman da na yi da marigayi a wad’ancan shekaru, na same shi gawurtaccen d’an jaridar da yake matuqar son aikinsa kuma yake muhimmantar da harshen Hausa. A wurinsa na koyi abubuwa da dama da suka shafi rubutun jarida na Hausa a aikace, kama daga rubuta ra’ayin jarida (editorial), maqala (article), da rahoto (news report). Kazalika na koyi yadda ake hira (interview) da manyan qasa. Marigayi ya koya min yadda ake jefa wa manya tambayar qurulla ba tare da shakka ba.
Ban da harshen da zan iya siffanta hikimarsa a rubutun Hausa a wannan lokaci da idanuwana ke zubar hawayen rashin wannan MAIGIDA nawa, illa iyaka kawai in ce mai son gane haka ya duba litattafansa da maqalunsa a jaridar AMINIYA da shafinsa na Facebook, lallai tabbas za a gane harshen Hausa ya yi babban rashi da rasuwar Mahmoon Baba-Ahmed.
Allah ya nauwara makwancinsa!

LEAVE A REPLY