Daga Aliyu Jibiya
Wannan wata baiwar Allah ce, wacce ta shekara ashirin tana kula da yaran da ake zubarwa a titi; sai ta dauke su ta shayar da su kamar ita ta haife su. Idan suka yi wayo ta sa su makarantun Islamiyya da na Boko har sai sun yi jarrabawar WAEC da NECO; daga baya idan mata ne, sai ta auras da su, Idan Maza ne, sai ta Ba su jari ta yayesu.
A bisa wannan dalili ne KUNGIYAR MURYAR TALAKA TA KASA, RESHEN JIHAR ZAMFARA, ta nemo wannan baiwar Allah ta kuma karrama ta! An yi wannan gagarumin biki ne a garin Gusau, jihar Zamfara.
Na halarci wannan biki kuma na Sami damar zantawa da Hajia BALARABA, kuma gaskiya, labarin ta yana cike da abubuwan ban tausayi, musamman idan aka yi la’akari da matsalar rikon gida da ciyarwa ga Mutumin da Ba albashi gareshi Ba, kuma Ba wata kwakkwarar sana’a ya ke da ita Ba!
Babu shakka labarin Hajiya BALARABA ya girgiza ni a lokacin da Na Kai ziyarar-Gani-da-Ido a gidanta da ke Tankin Ruwa, Gusau. Na tausaya mata, kuma Na tausayawa yaran da ta ke riko, kuma ta ke dawainiya da su.
Wannan baiwar Allah tana yin abincin sayarwa, amma saboda marrar yau, jarin ya tafi wajen kula da gida. Saboda haka tana bukatar tallafi da agaji na Al’ummah. Domin ko Leda Guda ta pure water aka taimaka mata da shi, yaranta sai su yi maganin kishirwa. Allah Ya taimaki dukkan Mai taimakon bayinSa, Ameen!
Domin neman karin bayani, za a iya samunta a wannan lamba (08067767667)

LEAVE A REPLY