Lawal Adam Gangara
Daga Lawal Adam Gangara
Tun farko kuskure ne Gwamnati ta fara kurarin zata kori duk wanda bai samu sakamakon da take so ba, domin ita Gwamnati uwace wadda take nemawa dukkan ‘ya ‘yanta mafita. Ba saka su cikin tsanani da damuwa ba.
Ya kamata Gwamnati ta dauki matakai kamar haka,  akan waɗanda suka kasa samun kashi 70 cikin 100.
1. A cikin su Akwai waɗanda sun kusa shiga shekarun gama aiki, to, irin waɗannan sai a sallemesu a basu haƙƙoƙin su. An hutar da su kenan.
2. A cikin su akwai waɗanda za’a iya mayarwa makaranta sai Gwamnati ta taimake su, ta maida su karatu, su samu Ilimi da sanin makamar koyarwa zuwa wani lokaci sai su dawo suci gaba da aikin su.
3. Akwai ayyuka da yawa a Gwamnati, wanda bai dace da koyarwa ba sai canza shi zuwa wani wajen da ya dace da shi. Koda gadin gandun daji ne kuwa.
4. Gwamnati ta ƙirƙiro wasu shirye shiye kamar Noma, Kiwo, Kana nan sana’o’i da sauran su (Musamman ga mata) a horar da su akan waɗannan abubuwan, sannan a basu dukkkan abinda ya kamata na taimako.
Amma kora ba mafita bace kamar yadda barin wanda bai cancanta yayi koyarwa cikin aikin koyarwa ba.

LEAVE A REPLY