Marigayi Malam Aminu Kano

Daga Anas Saminu Jaen

Likitan siyasa Arewacin Najeriya Marigayi Malam Aminu Kano, Allah ya gafarta masa tare da magabatan mu. yake cewar shin ya za a yi mu iya zama da junan mu, mu gane mai son mu da kuma dalilin da yasa yake son mu ko kin mu. Ya kuma za mu zauna da junan mu domin mu ci amfanin wannan zama tare.

Ga mu kowa dai a gida daya muke amman kowa yasan dakin uwar shi, kowa yai takama da nasa idan an hadu a kasuwa a gaisa ai zarafi, idan an hadu a majalissa a gaisa ai zarafi.

Akwai masu kashin munduriki Allah ya zabo su sune sama da sarakuna, suka ce sai sun wulakanta mutane Abun da kaf Allah baya so shi ne wulakanta mutane, mutuncin mutun shi ne babbar magana.

Malam ya ce idan sun dunga muma mun dunga ba za mu fasa ba bakin rai bakin fama, matasa sai mu yi koyi da irin siyasar su Malam Aminu Kano ba mu ringa jefa kawunan mu ga halaka da siyasar cin mutunci ba domin birge wadanda muke so, Adawa a siyasa ba karya ba ce amman sai a ringa ta ilimi da hankali.

Siyasar yanzu ta sha bamban da irin yadda su Malam Aminu Kano suka koyar da mutane a zamanin su, amman saboda rashin kunya kowane dan siyasa a nan arewa sai ringa ikirarin yana koyi da Malam Aminu Kano duk da shi bai taba yin ko yin shugabanci da sunan jagorancin siyasa ba, ya dai taba rike minista sadarwa dana lafiya zamanin shugaban kasa Yakubu Gawon abun da yasa ya bijirewa wannan gwamnatin ta soja ya zama dan gwagwarmayar kwato hakki da yancin mutan arewa tare da wayar musu da kai akan tsarin mulki kowane iri ne har aka shigo harkar siyasa gadan-gadan.

Wani lokaci Malam Aminu Kano yana kan Duro yana lakca sai ake tambayar sa menene bambancin mulkin soja da mulkin farar hula sai ya ce mulkin soja idan kaga an yi barna sai a hanaka ka fada to dan haka komai lalacewa gara mulkin farar hula da mulkin soja, da daman gaske ‘yan siyasa sun dare da Malam Aminu Kano sun zama wasu a siyasa amman ko kadan basa kwatanta hali irin nasa illah nadiran.

Mafiya yawan masu tutiya da halayan Malam Aminu Kano sune da yin sata ta fitar hankali, sun bar mutanan da suke mulka babu ilimi ingattacce, harkokin lafiya a Asibitoci sun yi karanci, ga matsalar rashin abun yi a ko ina cikin fadin kasar birni da kauye, uwa uba matsalar tsaro.

Amman duk da haka ‘Yan Nanjeriya Waliyaine domin akwai su da saurin yin “YAFIYA DA YADDA” ga ‘yan siyasa wadanda muka damkawa amanar wadancan abubuwan, kuma basa ganin haka kullum kara koyo dabarun azaftar da mutane suke yi, har yanzu mutanan mun kasa ganewa idan kuma mun gane to kwadayi ya hana mu bujirewa.

A cikin magoya baya an bar mu da kumfar baki a cikin gari da cin mutuncin junan mu wannan shi ne yana yin siyasar arewa gamu bamu da tsari balle kuma hadin kai daga manyan mu zuwa yaran mu, Babu abun takaici mutane suna Unguwa daya da suna yin sallah tare amman suna gaba da juna kan wani dan siyasa wanda bai san darajar su ba, Makarantar ‘ya’yan su daban da tamu, Asibitin su daban da naka sun samawa ‘ya’yan su aiki kai kuma sun barka da kwalin sakandire a hannu ba bu damar ci gaba saboda kowa ya yadda “Siysa Ita Ce Sana’ar Da Tafi Kowacce Kawo Kudi” su kuma ‘yan siyasar sun gane hakan shi ne suke azaftar da mu a hakan. Ko Yaushe Matasa Zamu Ko Yi Tirjiya Da Naki A Siyasa Kamar Yadda Marigayi Malam Aminu Kano Ya Koyar Da Iyaye Da Kakanni A Nan Arewa.

Idan muka duba Kano ita ce cibiyar siyasa kasuwancin arewa amman har yanzu ana cutar da mutane ta dalilin siyasa kuma mu da ake mulka bamu damu ba, kuma a ce a nan aka fi yawan samun rikici tsakanin gwamna da mataimakin sa tun ba yanzu ba ko da yaushe idan an samu canjin gwamnati hakan ita ce ke faruwa, Dole mu da ake mulka sai mun nuna damuwar mu saboda jihar mu ce mu ake mulka mu ake yiwa aikace-aikace abun mu zai fi shafa dan haka bai kamata mu biye musu ba mu mabiya damu suke takama, Da wannan damage zan yi kira ga ‘yan uwana matasan jihar Kano kada ku saka kanku ga halaka musamman yanzu saboda gwamna Abdullahi Umar Ganduje ko Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Idan kuka yi tunani ‘ya’yansu irin su Muhammad Umar Ganduje da Mustapha Rabi’u Kwankwaso na can cikin daula sun bar ku! Da su da iyalan su Allah Ta’ala ne kurum yasa tsakanin su tare muka gansu, duk ruru wutar rikin siyasar da ake yi laifin magoya baya ne.

Ya Kamata Matasa Mu Yi Hankali Kar Mu Jefa Kan Mu Cikin Rudanin Siyasa, Kuma Mu Nemi Tarihin Abun Da Ya Faru A Siyasar Janhuriya Ta Farko Ta Biyu Zuwa Janhuriya Ta Uku Game Da Siyasar Kano : Abin da ya dace shi ne mu fifita son zaman lafiyar jihar Kano da Najeriya fiye da nunawa ‘yan siyasa soyayya komai matsayin su da mukamin su a gwamnati, ‘yan uwa daga tsagin Gandujiyya da Kwankwasiyya da sauran bangarorin siyasar jihar Kano ku yi hakuri kowa ya rike ra’ayin sa a zuciyarsa mu zauna lafiya da juna domin ci gaban jihar mu da kasar mu gaba daya.

 

LEAVE A REPLY