Shugaba Muhammadu Buhari
Daga Ado Abdullahi
Hukumar da ke kula da ƙiyasin talauci a ƙasashen duniya ta bayyana cewar Najeriya nan da shekaru 32 masu zuwa wato a shekarar 2050 za ta zama ƙasa ta uku a yawan jama’a a duniya inda za ta maye gurbin ƙasar Amurka wacce yanzu ta ke a matakin ta uku. Wato Nigeria za ta biyo bayan ƙasashen Indiya da Chaina. A lokacin kuwa yawan jama’ar ƙasar nan zai haura mutum milyan 400 !
Kamar yadda rahoton ya nuna a watan Fabrairu da ya wuce Najeriya ta zarta ƙasar Indiya yawan matalauta. Domin a halin da ake ciki yanzu ƙasar nan tana da mutane milyan 80 da suke cikin matsanancin talauci (wato masu zama hannu baka hannu ƙwarya), wanda yawansu ya kai kashi 42.4 na yawan al’ummar ƙasar nan.
Ita kuwa Majalisar ɗinkin duniya ta bayyana zama cikin ƙangin talauci ga duk mutumin da ya ke rayuwa a bisa samun ƙasa da dala 1.90 wato kwatankwacin naira 700 kenan a rana.
Majalisar ta ƙara da cewar dole ƙasashen duniya su yi ƙoƙari wajen cire aƙalla mutane 90 daga matsanancin talauci a duk minti ɗaya a duniya domin samun ganin duniya babu mutane masu baƙin talauci da za su rage zuwa nan da shekara ta 2030. Sai dai kash, misali mu a nan Najeriya binciken ya nuna maimakon fita daga matsanancin talaucin, duk minti ɗaya mutane kusan bakwai ne suke kara afkawa cikin baƙin talaucin.
Lallai akwai tashin hankali a gaban ƴan Najeriya yadda yawan jama’a ya ke fin ƙarfin cigaban tattalin arziƙin ƙasar. Dole ɗaiɗaikun ƴan ƙasa da gwamnatoci a dukkanin madafun iko su tashi tsaye domin ganin yadda za a daidaita yawan al’umma da tsarin tattalin arziƙi.
Babbar matsala ita ce mu anan arewacin Najeriya inda muke da ƙarancin ababen more rayuwa, mune muke da ƙarancin arziƙi ga ɗaiɗaikun al’ummarmu da kuma tsabagen yawan jama’a marasa kataɓus ga cigaban yankin.
A cikin watan Maris ɗin nan ne,
Hukumar Abincin ta Majalisar Ɗinkin Duniya tare da Shirin Samar da Abinci na Duniya WFP sun yi gargaɗi cewa ƙarancin abinci zai shafi mutane miliyan
 3.8 a jihohi 16 a arewacin Najeriya da Abuja, babban birnin kasar nan.
Jihohi 16 din sun haɗa da Bauchi da Benue da Gombe da Jigawa da Plateau da Niger da Kebbi da Katsina da Kaduna da Taraba da Sokoto da Kano da Yobe da Borno da kuma Adamawa.
A bisa ga rahotannin nan da ma wasu da ba a kawo anan ba, lallai ƙasar nan akwai barazana ta ƙarancin abinci a ƴan shekaru masu zuwa wanda zai iya haifar da rashin samun cikakkiyar kulawa daga mahukunta da kuma waɗanda ma alhakin kulawa da tarbiyyar iyalensu ya wajaba a gare su. Haka zai haifar da yawan tashe-tashen hankula tsakanin mabanbanta addinai da faɗan ƙabilanci da ɓangaranci tsakanin al’umma. Domin shi talauci gami da rashin aikin yi kan sabbaba tashin hankali a ƙasa.
Anan Arewa akwai ƙarancin ayyukan yi ga matasanmu waɗanda suka gama  ilmin bokon da ma waɗanda ba su yi ba. Ga tarin ƙananan yara marasa tabbas a kan tituna musamman mabarata da sunan neman ilmin addini, ga almajirai, gajiyayyu da masu naƙasa duk sun cika titunanmu suna gararamba. Yanzu hatta matan aure waɗanda mazajensu ko dai ba su iya ciyar da su ko sun gudu sun bar su, Suma sun shiga harkar nan ta bara. Ga yara marayu waɗanda babu wani tsari a ƙasa domin kawo musu tallafi su ma sun bi sahu.
Lallai wannan ƙalubale ne wanda matuƙar ba mu tashi tsaye ba toh nan da waɗancan shekaru 32 masu zuwa ba mu san inda yankin arewacin Najeriya zai shiga ba.
Wajibi ne mu lalubo hanyoyin da za su kawo mana cigaba mai ɗorewa wanda jikoki za su yi alfahari da mu nan gaba.
A rubutu na gaba zamu yi nazarin menene mafita ga yawan al’umma da kuma talauci duk a lokaci guda a Arewarmu da ma ƙasa baki ɗaya ?

LEAVE A REPLY