Muhammadu Buhari
Daga Ado Abdullahi
Hausawa kan ce Wuya, ko da magani ba daɗi ko kuma su ce, Wahala tallar turmi, wato duk ta inda ka biyo ita wuya ko wahala ba daɗi gareta ba. Wato babu jidali a ce mutum an bashi aikin kare ƙarya ko burun burun da aka yi domin yaudarar al’umma.
Yau sama da shekaru uku da wannan gwamnatin ta Buhariyya ta shafe tana mulkin ƙasar nan kuma ba tare da ganin wani abin a zo a gani ba. Domin dai ta shafe shekaru biyu da rabi tana zargin gwamnatin baya ta PDP da tsunduma ƙasar nan cikin mawuyacin hali. Zargin da su kaɗai suke kiɗansu suke rawarsu domin dai shi talakan da ake mulkin domin sama masa sauƙi da walwalar rayuwa babu abin da ya ke ji sai baƙar wahala saboda rashin tsari da damalmala harkokin tattalin arziƙin ƙasar nan.
 Daman sun ce jiki magayi to lallai jikin talaka yana gaya masa,  domin dai yasan jiya tafi yau. Bahaushe kuma yana cewa kowa ya tuna bara bai ji daɗin bana ba.
Sanin wahalar kare wannan gwamnatin ne yasa shi kansa shugaban ƙasar aka rawaito yana cewa aiki ne mai wahala wani ya kare shi ko ya kare gwamnatinsa. Ya faɗi haka ne a makon jiya lokacin da ya karɓi baƙuncin ƙungiyar ƴan jarida masu goyon bayan Buharin a fadar shugaban ƙasar.
Jawabin shugaban ƙasar yana tabbatar da gazawarsa wajen biyan buƙatar al’ummar da suka zaɓe shi. Domin kullum alƙawarinsu ba cika yake ba sai kuma ƙaro wasu alƙawurarran suke babu ƙaƙƙautawa.
Kirana ga masu kumfar baki da zage-zage domin an faɗi gazawar gwarzonsu shi ne ya kamata su bi a hankali su sani duk wanda ya  more inuwar gemu bai kai maƙogwaro ba. Domin hatta uwargidan shugaban ƙasa Hajiya Aisha Buhari sai da ta yi adawa da yadda ake tafka kura kurai a wannan gwamnatin. Idan kuma so ne, ba dai za ku ce kun fi ta ƙaunar Buharin ba. Idan kuma kwasar romon democraɗiyyar ne ba ku kai ta ba, ita ce ajin farko domin ita har ƴarta ta INDIMANCE abinta duk kuma dalilin shiga gidan gwamnatin Aso rock ne.
Saboda haka wanda duk ya ɗauki aikin kare wannan gwamnatin ƙarya da gaskiya ya ɗauko tallar turmi…..

LEAVE A REPLY