Sheikh Bala Lau
 Daga Ado Abdullahi
Allah (Subhanahu Wata’ala) Yana cewa a cikin Al-Kur’ani mai girma, Suratu Al-Imran aya 104: “Kuma wata jama’a daga cikinku, su kasance suna kira zuwa ga alheri, kuma suna umarni da alheri, kuma suna hani daga abin da ake ƙi. Kuma waɗannan sune masu cin nasara”.
Mun iya cewa ƙasar Hausa da ma nahiyar yankin Afrika ta yamma gaba ɗaya, ba ta  samu wata tawagar al’umma wacce ta ɗabbaƙa aiki da waccen aya ba bayan tawagar Mujaddadi Shehu Usmanu Ɗanfodiyo sai kuma wannan ƙungiya ta Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa’iƙamatis Sunnah. Wacce ake yi wa laƙabi da IZALA ko JIBWIS.
An kafa ƙungiyar ne domin yaƙi da mugayen al’adu da Bidi’oi. Ya ƙi da ayyukan assha da tsibbace-tsibbacen bokaye, ƴan duba da ƴan bori waɗanda suka saɓa da karantarwar addinin Islama. Hakanan ƙungiyar tana faɗa da munanan aƙidun Ɗariƙun Sufaye da kuma masu iƙirarin Shi’anci a cikin al’umma da kuma uwa uba yaƙi da masu haɗa Allah da waninSa cikin bauta, wato masu  Shirka.
 Aikin Ƙungiyar ne dai: ɗora al’umma bisa tafarkin tsira da dawowa kan addinin ainihi kamar yadda Annabi (Sallahu Alaihi Wassalam) ya karantar da sahabbansa, su kuma suka yaɗa shi ba tare da gurɓata shi ba.
Ayyukan ƙungiyar ya kama daga wa’azi saƙo-saƙo, buɗe makarantu domin karantar da yara, manya mata da maza ga kuma dubban masallatai a ƙarƙashinta.
Babban abin sha’awa shi ne yadda a ƴan shekarun nan ƙungiyar ta yi wani namijin ƙoƙari inda ta buɗe tashar talabijin ta ƙashin kanta a tauraron ɗan Adam mai suna MANARA TV. Wannan namijin aiki ya zamanantar da ayyukan ƙungiyar da sauƙaƙawa milyoyin al’umma damar samun sauraron karatuttuka cikin sauƙi. Da kuma samun sauƙin aika  saƙo da manufofin ƙungiyar a duk fadin duniya a ɗan ƙanƙanin lokaci.
A cikin tsarin zamanantar da ayyukan ƙungiyar ne da kuma faɗaɗa tunani, ƙungiyar ta fara shirin karɓar taimakon fatun layya daga ɗimbin jama’ar Musulmi a duk faɗin ƙasar nan. Shirin ya cimma nasara ba kaɗan ba tun lokacin da aka fara shi. A ƙarƙashin wannan tsari, ƙungiyar ta samar da wani katafaren masaukin baƙi a babban birnin tarayya wato Habuja. Wanda yin haka ya ragewa ƙungiyar wahalar kama ɗakunan baƙi masu ɗan karen tsada a duk lokacin da hidimar taruka ta same su a birnin na Habuja.
Haka yanzu aiki ya yi nisa na gina sakatariyar ƙungiyar da asibiti da kuma masallacin juma’a duk dai a garin Habuja.
Babban abin farin ciki kuma shi ne samar da wani katafaren fili da ƙungiyar ta yi a garin Hadeja da ke jihar Jigawa inda ake sa ran zata kafa wata katafariyar jami’a ta musulunci a ƙasar nan. Wannna namijin ƙoƙari bayan samarwa ƙungiyar ƙuɗaɗen shiga, zai taimaka wajen samar da ayyukan yi ga ɗaruruwan membobinta da suka kammala wasu manyan jami’oi na ƙasar nan dama ƙasashen waje. Haka zai bayar da damar ɗaukar ma’aikata masu gudanar da jami’ar .wannan ba ƙaramin taimakawa yunƙurin gwamnatoci na samar da ayyukan yi ga al’umma zai yi ba.
Amfanin wannan jami’a ba zai bayyanu a ɗan ƙaramin rubutu irin wannan ba. Domin kowa yasan irin faman da ɗalibai suke yi wajen cincirindon neman guraben karatu ciki da wajen ƙasar nan.
Babban abin da al’umma ya kamata su yi shi ne zage dantse, da tashi tsaye wajen bayar da taimako kamar yadda suka saba a baya, musamman wajen bayar da fatun layya ga wannan ƙungiya mai albarka domin kammala wannan aiki da aka tasamma.
Duk da kasancewar ba za a rasa masu ƴan ƙorafe-ƙorafe ba wajen tafiyar da wasu ayyuka na ƙungiyar amma dai shugaɓannin ƙungiyar suna ƙoƙari daidai gwargwado wajen aiwatar da ayyukan da aka ɗora musu. Kasancewarsu ba Annabawa ba, za su iya yin kuskure a wasu lokuta, amma dai alhamdulilah zamu iya cewa daidai ɗin ya rinjaya.
Muna kyakkyawan fatan ganin manyan asibitoci da ƙarin wasu jami’oin nan da ƴan shekaru masu zuwa daga wannan katafariyar ƙungiya ƙarƙashin babban jagora Ash-Sheik Abdullahi Bala lau.

LEAVE A REPLY