Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Daga Fatuhu Mustapha
Shekarun baya, shugaban babban bankin Santara (Central Bank) Malam Charles Soludo, ya bayyanawa duniya a wani taron duniya da akayi a Birnin Dutse na jihar Jigawa cewa;  “Matsalar fatara da talauci, matsalar arewa ce kawai a Nigeria”. Duk da irin cece-cece -kucen da batun nasa ya jawo, amma kusan duk wani mai hankali ya tabbatar da hakan akwai kamshin gaskiya acikin batun babban shugaban bankin. Sai dai abin tambaya anan shine; shin mai ya jawo hakan?
Na daya dai babban dalilin talauci a arewacin Nigeria yana da nasaba da irin yanayin jagoranci da arewa ta samu kanta, tun bayan da shugaban kasa Alhaji Shehu Shagari ya dauki matakin tsuke bakin aljihun gwamnati (austerity measures) da kuka matakin Kowa -ya-ji-a-jikinsa wato (SAP) da gwamnatin Babangida ta kawo, tattalin arzikin arewa , musamman bangaren masanaantu ya shiga wani mummunan yanayi. Wannan yanayi ya janyo rufe kamfanoni da dama, wadanda suka janyo rashin aikin yi ga magidanta da dama, hakan ya sanya mafi akasarin iyalan Hausawa a halin ni-ya-su.
Da yawa daga cikin Attajirai da ke da masanaantu a arewa suka chanja akala daga kafawa da kula da masanaantunsu zuwa kwangila.
Samu da tashin farashin man fetur a shekarun 1970s ya janyo attajiran arewa da ke hada hadar cinikin kayan noma, sun watsar sun koma sanaar fetur da kuma kwangila. Wannan ya sanya kusan noma da a da ya samar da mafiya akasarin masu kudi da attajiran arewa , ya zama wani abin kyama bawai kawai ga masu hannu da shuni ba, har ma ga talakawa mazauna karkara. A wannan lokaci gwamnati ta fara ja da baya wurin zuba jarinta da kudadenta a harkar noma, ta koma zuba makudan kudade a harkar man fetur.
Halin biris da gwamnati tayi da aikin gona, da kuma nuna ko in kula da kasuwanci kayan albarkatun gona da kuma cibiyoyin nazarin noma , shi ya sanya mazauna karkara suka fara shigowa birane domin neman abinyi. Wanda hakan ya haifar da matsalar barace – barace da hauhawar laifuka a birane.
Gwamnonin arewa da ya kamata ace sun maida himma, tare da wakilan arewa a majalisun tarayya, sun taimaka wurin habaka ayyukan gona domin tallafawa tattalin arzikin jihohinsu, sun zama basa komai illa gafiya tsira da na bakinki, a duk lokacin da suka samu mukamai. Sun manta da cewa, a sama da shekaru 70 da suka gabata kafin man fetur ya zama wata tsiya a duniya, noma ne ke rike da tattalin arzikin arewacin Nigeria.
Babban dalilin da ya sanya haka kuwa shine; tsarin nan na fedaraliya wanda ya bada damar lallai a ringa raba tattalin arzikin kasa, ga kowa da kowa (fiscal federalism). Wannan ya sanya jihohin arewa sun zama cima – zaune, basa bada gudunmowar komai a Nigeria sai dai su jira a tara kudin man fetur a raba musu. Hakan ne ya janyo mana gori daga mutanen kudu, da suke kallon arewa a matsayin nauyi ne kawai a wuyansu da suke fatan su samu damar da zasu yakice.
Babbar illar da lalacewar harkokin aikin gona da masanaantu ya janyowa arewa shine; jihohin na rashin haraji mai kauri, wanda kusan zai iya linka na man fetur da ake sammmusu a kowane karshen wata, tun bayan da majalisar tarayya ta amince da tsarin nan na ware kaso 13 cikin dari na kudaden man fetur,  kuma a mika su ga jihohin da ake hakar man (13% derivation formula).
Hakan kuma ya janyo rashin aikin yi ga dimbin matasan arewa, wadanda a kullum yan siyasa ke yaudara da samarwa da aikin yi in suka zabe su. Wannan ya sanya matasan arewa sun zama wani alakakai ga zaman lafiyar kasar, wanda shine makasudin yawan tashe-tashen hankula da fituntunun dake addabar yankin.
A saboda a yanzu dai kusan duk wani gurbi na aikin gwamnati ya cike, sai dan abunda ba a rasa ba. Matukar ba masanaantu aka samu a Arewa ba, ba yadda gwamnati zata samar da aikin yi ga wadannan matasa.
Amma duk da wannan, su kansu masu aikin yi a arewa, wanda mafiya akasarinsu maaikatan gwamnati ne, ko banki sai kuma yan tsiraru dake aiki a tsirarun masanaantu dake yankin, su kansu acikin talaucin suke, kamar yadda zamu gani anan gaba. Domin in an kalli abin da idon basira, zaa fahimci cewa, mutum uku muke wa aiki; Yarabawa, inyamurai da kuma yan kasuwar China da Thailand. Bari mu ga yadda abin yake.
A yau in ka dauki albashi, ka Riga dama ka sa a ranka ba zaka ci shinkafa yar Nigeria ba, don haka yar waje da aka kawo daga Brazil ko Thailand zaka saya, cinikin da kayi dai, shi zaa canja zuwa dollar a kara maidawa yan kasuwa da manoman kasar Brazil ko Thailand su kuma su kara zuba kudin a harkar nomansu su kara bunkasa shi, manomanku kuwa ko oho.
Kusan a kayan masarufi da ake amfani da su yau da kullum, in ka dauke hatsi , mai da nama, dukkan abinda zaka saya Yarabawa ne ke yinsa. Su zaka yiwa cinikin, harajin kuma na kayan masarufi wato (VAT) gwamnatocinsu zaa baiwa, ba abinda gwamnatin da kake yiwa aikin zata samu, sai dan abinda ta yankar maka na haraji. Daga karshe dai gwamnatin Ogun da Lagos ne zasu kwashe harajin, yan kasuwarsu kuma su kwashe cinikin. Wannan ya hada da maggi, sukari, madara, sabulu, omon wanki da sauransu.
Wannan haka yake a bangaren kayan mota da kayan gini da sauransu. Wanda mafi akasarin masu saida su inyamurai ne.
Koda kayan Dangote ko Abdussamadu, in an lura dukkan masanaantunsu a kudu suke, kuma harajinsu duk can yake tafiya.
Wadannan dalilai su suka janyo talauci yayi mana katutu a arewacin kasar nan.
Matukar gwamnoninmu da yan siyasarmu basu maida himma a wurin aikin gona da masanaantu dake alaka da albarkatun gona ba (agro allied industry). To kuwa kullum a talauci zamu dawwama.
Allah ya kawo mana mafita!

LEAVE A REPLY