Bello Galadanchi
Idan na baka mamaki, to nima ka bani mamaki. Ba’a fafan gora ranar tafiya. Idan ka shirya wa Monday, to mene ne abun fargabar ta? Kasala ne? Ko ka manta kasala cuta ne, kuma rashin ta nasara ne? Batun gaskiya duk inda ake hangen nesa a kowace rana, da aiki babu ganda, da rashin son zuciya, da fahimtar juna to ina son kasancewa a ciki. Monday kuwa ta kasance ranar da ake haduwa da jama’a musamman bayan hutawa a karshen mako. Yanzu ga wani dan guzuri nan domin taimaka wa matashi wajen tsayawa akan kafafun sa.
Kafin nayi nisa, ina so nayi tuni; duniyan nan kullum canzawa take yi, kuma bata jiran kowa. Idan yau ka share sa’o’i tara kana bacci, wani shida yayi, sannan yayi amfani da ukun da kake bacci wajen yin wani abu da zai bunkasa rayuwar shi ya fi ka samun ilimi, ko ya fi ka dabaru, ko kwarewa, ko samun kudi, ko fahimtar sirrin yau da gobe. Duk matashin dake so ya bunkasa kan shi, to akwai abubuwa 5 da ya kamata ya mallaka:
1. BURI: Duk matashin dake da buri, jama’a sun fi sha’awar shi, sannan yana harzuka mutane tare da samun dama iri-iri daga bil adaman da yake haduwa da su. Idan kana da buri, to kai abokin kowa ne.
2. DARAJA: Daraja abu ne da kowa yake so ya kara. Idan abokai ne da kai, ko aiki, ko sana’a, to idan har ka darajanta kanka, to za’a kusance ka, kuma za’a saka ka a inda darajar ka zata yi amfani. Kayi kokarin kware wa a wani abu, ko ka kammala karatu. Bugu da kari, halin ka ya zama mai kyau, duk wadannan zasu kara maka daraja sannan zaka gina wa kanka gimshikin rayuwa mai karfi.
3. IYA MAGANA: Matasa masu yawan gaske suna fama da matsalar rashin iya bayyana abunda ke cikin zuciyarsu a saukake. Wadannan abubuwa sun kama daga kwarewar su, hikimar su, irin burinsu da aikace-aikacen da suka yi a lokacin da suke neman ilimi. Nasara a rayuwa ba farilla bace, saboda haka idan har kana so, dole sai ka mike ka nema. Kuma a lokacin da kake nema, akwai miliyoyi kamar ka da suke nema kuma basu samu ba. Sai ka zage damtse ka kware a magana, kuma ka fadi gaskiya.
4. KWAREWA: Duk dabbar da bata da dabara a cikin dawa, to kuwa sunan ta gawa. Duk mutumin da yaki kwarewa wajen yin wani abu a rayuwa, to shima sunan sa gawa, saboda da shi da gawar marabar su kadan ce. Idan baka kware a wani abu ba, to baka da daraja. Idan baka da daraja, babu wanda zai yi sha’awar ka ko yaso yayi muamalla da kai. Jama’a sun fi kaunar gwal saboda yana da daraja. Kar ka zama dutse, ka samu wani abu ka mayar da hankali akai ka iya shi yadda ya kamata. Kar ka yi ta kame-kame a rayuwar ka.
5. NEMAN ILIMI: Wannan yana da matukar amfani. Ko kai Farfesa ne, to idan har kana so ka cika mutum, kuma ka cimma burin ka na rayuwa, to ka bude idanunka kullum wajen neman sani. Idan ka hadu da wanda ya san wani abu da baka sani ba, to ka girmama shi, ka yi tambayoyi domin ya fahimtar da kai. Ka nemi littatafai ka karanta. Ka binciki duk abunda yake baka sha’awa. Kar ka dogara akan karatun makaranta kawai, a’a, ka hau yanar gizo ka yi bincike. Ka samu masani yayi maka karin bayani. Ka zama mayunwaci a neman ilimi har karshen rayuwar ka.
Zaman duniya ba abu ne mai sauki ba. Idan ka zauna zaman jira ba tare da inganta rayuwar ka ba, to a haka zaka kare jama’a basu darajanta ka ba, kuma kaima baka darajanta kan ka ba. Allah Ya kiyaye mu, kuma Ya bamu rayuwa mai albarka.

LEAVE A REPLY