Malam Salihu Sagir Takai
Daga Bashir Yahuza Malumfashi
Daga yadda al’amuran siyasa ke gudana  a yau a Jihar Kano, akwai yiwuwar Malam Salihu SagirTakai ya yi tasiri a takararsa ta Gwamnan Jihar Kano a zab’e mai zuwa a 2019.
Al’umma suna kallonsa a matsayin mai mutunci, mai kamala kuma mai addini. Haka kuma ana ganinsa a matsayin mai biyayya, musamman yadda yake tafiyar da alak’arsa da tsohon Gwamna Malam Ibrahim Shekarau har bayan sun sauka daga mulki.
Malam Sagir matashi ne, mai ilimi tudu biyu, na zamani da kuma na addini. Wannan za ta iya ba shi damar samun tagomashi daga matasa masu ilimi, sannan kuma zai iya samun tagomashi daga manya.
Akwai rigima da gagarumar matsala tsakanin Sanata kuma tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamnan Jihar Kano na yanzu, Abdullahi Umar Ganduje, matsalar da idan ba su daidaita kansu ba, to za su iya yi wa kansu illa a siyasance a zab’e mai zuwa a 2019. Kwankwaso na iya amfani da tagomashinsa da mabiyansa, ya lalata wa Ganduje al’amura, yadda zai yi asarar komawa kujerarsa. Shi ma Ganduje na iya amfani da damarsa ta kujerar Gwamna ya lalata wa Kwankwaso damar komawa Sanata, idan ya nemi haka.
Duk da cewa akwai matsala tsakanin Malam Ibrahim Shekarau (Ubangidan Takai) da Kwankwaso a siyasance, Malam Sagir Takai na iya k’ulla alaka da Kwankwasiyya domin cin ma manufa. Domin ita siyasa, kamar yadda masana suka ce, ba ta da dawwamammen abokin gaba ko dawwamammen abokin arziki – buk’atar d’an siyasa ita ce, ya cin ma manufa ko tare da wane ne kuma ta kowace hanya mai b’ullewa.
Kasancewar Takai ya kafa kwamitin mutum 15 domin shirin tunkarar 2019, akwai yiwuwar su yi aikin sama masa kwarjini da mabiya daga sassan al’umma daban-daban, musamman ganin cewa cikin kwamitin har da jajirtaccen malamin jami’a, Dokta Bashir Shehu Galadanchi da Barista Faruk Iya Sambo da Hon. Ubale Jakada Kiru da sauransu.
Wannan kwamitin na iya samun nasarar k’ulla sahihiyar alak’a da gidajen Sarauta, Malaman Addini, Attajiran ‘Yan Kasuwa, Malaman Jami’a, K’ungiyoyin ‘Dalibai da na Matasa da sauransu. Kasancewar akwai Hajiya Aishatu Mai Jamaa a cikin kwamitin, a matsayinta na fitattar ‘yar siyasa, tana iya samo wa Takai k’ungiyoyin mata.
Babu shakka, harkar siyasa a Jihar Kano a 2019 akwai kallo! Allah Ya zab’a wa al’umma mafi alheri, amin!

LEAVE A REPLY