Daga Mahmud Isa Yola

Menene zai fi baka mamaki sama da haduwar Atiku da Obasanjo (sun shirya) in ba haduwan Sheikh Ahmad Gumi da Rabaran Matthew Kukah ba?

A ilimin kimiyya, haduwa na nunufin gamuwar kwayoyin sinadarai (ions or molecules) sakamakon sanannen alakar kasantuwa dake tsakanin su (lasting attraction between Atoms) saboda zama “chemical compound”.

A ilimin fasahar dan Adam, haduwa yana nufin samar da alaka tsakanin mutane biyu ko fiye, ko kungiyoyi biyu ko fiye, saboda cin ma manufa da dukkan wadanda zasu samar da alakar suke dauke da shi.

A ilimin fasaha (technology) haduwa yana nufin karfin gamuwa (attraction force) tsakanin sinadarai (atoms or ions) don samar da daya daga cikin “coordinate, covalent, ionic metallic ko kuma polar bond”.

Saboda haka haduwa na nufin kazo, in zo, shi ma yazo don mu cin ma manufa guda daya kenan AMMA sai idan banbancin mu bai kai karfin manufar da muke so mu cimma a haduwa ba. Amma idan akwai banbanci mai karfi a tsakani, wanda ya fi karfin manufar da ake so a cin ma yayin haduwa.

Abunda nake so na ce shine: idan har akwai abunda zai sanya Obasanjo, wanda watanni biyu da suka gabata yake gayawa ‘yan Jarida cewa idan ya goyi bayan Atiku bazai samu gafarar Ubangiji ba, lokaci daya ya amince da takarar sa, kari akan haka ya hada Rabaren Matthew da Sheikh Ahmad,wannan ba karamin manufa bane.

Ina gani a bayyane manufar take, manufar siyasa. Siyasa kuma na kawar da APC daga mulki. Ko ince kawar da Buhari.

LEAVE A REPLY