Mas’alar Mamayar da Yahudu su ka yi wa Masallacin al-Aqsa da Birnin Qudus da kasar Palasdinu ita CE mas’ala mafi ciwo da musulmai su ka hadu da ita tun bayan faduwar inuwar da ta hada musulman duniya wuri guda (khilafa) a shekarar 1923 a Turkey.
Masallacin al-Aqsa shine alkiblar musulmai ta farko a zamanin Manzon Allah s.a.w, shine kuma bigire na uku mafi tsarki a wajen musulmi, bayan Masallacin Makka (Harami) da Masallacin Manson Allah (s.a w) da ke Madina (Taybatur Rasoul).
Kamar yadda ya ke wajibi mu kare Masallatan Makka da na Madina daga cutarwar dukkanin wani mai cutarwa, haka kuma ya wajaba mu yi aiki tukuru wajen kare Masjidul Aqsa daga cutarwar Yahudawa da jajircewa wajen ganin sai ya dawo hannunmu.
Ta hanyar karfi ne kadai za a iya dawo da masallacin al-Aqsa, kamar yadda da karfi aka kwace shi, Wanda hakan ke nufin cewa kashi 90% na nauyi na kan shuwagabannin musulmai domin su ne ke rike da madafun iko da sanin makamar yaki.
Idan aka yi rashin sa’a al’umma ta tsinci kanta a yanayi na rauni da fama da munafukan shuwagabanni masu hada kai da abokanan gaba kamar halin da mu ke ciki, to a nan wajen wajibin da ke kammu shine nuna matsi garesu da aiki tukuru wajen tarbiyyantar sabuwar al’ummar da za ta yi aiki domin maslahar al’umma, da cigaba da wayar da kan al’umma kan hakikanin matsalolinmu, da isarda duk wani tallafi da zai taimaka wajen raunata Abokin gaba.
A lokacin da Kiristocin (Crusaders) su ka mamaye Qudus a  karni na biyar bayan hijira, abubuwa biyu ne su ka faru:
Malamai su ka dau nauyin da ke kansu na tarbiyar al’umma tarbiyya ta hakika da gyara zuciyarta da sanya mata ruhi da kishin jihadi da kakkabe son duniya a zukatan malamai da dalibai da sauran matasa, Wanda wannan tarbiyyar ta dau kimanin karni guda cif-cif, kuma ita ta fitar da mutane irinsu Salahuddeen Al-Ayyuby da abokanan gwagwarmayarsa kamar yadda marubuta tarihi ke bayyanawa.
A lokacin da Salahuddeen ya zo ya tadda duniyar musulunci a rikirkice, musamman ta bangaren masu mulki, son duniya ya mamaye su, kusanta da mika wuya ga abokanan adawa ya zama abin kwalliyarsu, ga tsabar amfani da munafinci da dasisa da mulkin kama-karya. Wannan ya sanya ya fara bi ta Kansu , sai da ya murkushe su sannan ya Samu damar dawo da Birnin Qudus da masallacin al-Aqsa hannun musulmai.
Tabbas a yanayin da musulmai su ke a yanzu babu wani tasiri da talaka irina irinka za mu iya yi na daqo  da kudus a daidaiku, tunda ba mu mallaki madafun iko da na karfin soji ba, amma kuma za mu iya bada gudummarmu ta bangarori guda hudu:
Bangare na farko shine raya mas’alar a zukatan musulmai da wayar da Kansu kanana da yara Don su San cewa fa akwai mafi tsarkin bigire na musulmai na uku a duniya da ke hannun makiya Allah, domin Allah na iya amfani da wasu daga cikinsu wajen wannan aiki, kamar yadda yayi amfani da Gamji Sir. Ahmadu Bello Sardauna a baya, Wanda irin gudummawar da ya baiwa batun falastinu ba Dan kankani ba ne, za mu yi bayaninshi a rubutu na gaba InshaAllahu.
Bangare na biyu shine bangaren Tarbiya akan kyawawan Aqidu masu dauke da kadaita Allah shi kadai da ganin girman shi shi kadai da rashin ganin kwarjinin waninshi, da tawakkali gare shi, da mika wuya ga umurninsa, da kaunarsa, da jajircewa akan bin umurninsa da umurnin Manzonsa (s.a.w). Sa’annan a cusawa al’umma ruhi na jin izzar Musuluncin da su ke dauke da shi da jin karama da daukaka da nesantar kaskanci da cire tsammani da aiki tukuru wajen kokarin cimma manufofin da addinin musulunci ya zo da su a ban kasa.
Hakanan tarbiyyantar da  al’umma akan wajabcin hadinkai da nisantar rarrabuwa da kaucewa dabi’u irin na handama da babakere  da sonkai da jiji-da-kai da gyara alakokin da ke tsakaninmu da mu’amalolinmu. Alal hakika wannan bangaren shine jigon sirrin nasarar da jagororin musulunci na baya su ka Samu akan makiyansu.
Bangare na uku shine bangaren Nuna matsin lamba ga jagororinmu Don ganin lallai ne sun wakilci al’umma hakikanin wakilci a wannan batu, za mu yi haka ne t dukkanin wata hanya da ta dace, kamar Media, Majalisu, tuntuba ta kai tsaye da sauransu.
Amin.
Bangare na hudu shine akwai bukatar addu’oi ga wannan masallaci, da addu’a ga shuwagabannin kirki da kungiyoyin gwagwarmaya da makami da ke yankin falastinu, masu yi da gaske wajen ganin an kwato wannan masallaci da makiya ke najastawa. Hakanan akwai damammakin tallafawa masu yin zaman dirshen da Ribati a cikin wannan masallaci domin bada kariya gareshi .

LEAVE A REPLY