Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Ado Abdullahi
Adawa irin ta siyasa daga abokan hamayya ba baƙon abu ba ne a tafiyar dimocraɗiyya. Amma samun tirjiya ko buɗa ƙasa a ido daga waɗanda su ka taimakawa ɗan siyasa ya kai gaci, ba ƙaramar koma baya ba ce, a tsarin siyasa a ko’ina a duniya.
Shugaba Muhamamdu Buhari a makonnin nan biyu da su ka wuce ya sami manyan ƙalubale daga wasu jigajigai da za a iya cewa sun taka kyakkyawar rawa wajen ganin ya ɗare bisa shugabancin ƙasar nan. Cif Olusegun Obasanjo,  tsohon shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP wanda ya juyawa jam’iyyarsa baya a zaben 2015 inda ya marawa Buhari baya domin ganin an kayar da Shugaba Goodluck Jonathan a wancan zaɓe. Yanzu ya yi ‘mi’ara koma baya’, inda aka rawaito cewar, Obasanjon ya ce Shugaba Muhammadu Buhari yana sakaci sosai a ɓangaren tattalin arziki duk da koke-koken da ƴan ƙasar ke yi.
Cif Obasanjo ya bayyana haka ne kuwa a wata hira ta musamman da ya yi da BBC.
A cewarsa, “Akwai buƙatar ya kai ga mataki na gaba [a yaƙi da Ƙungiyar Boko Haram], amma ba tare da an yi watsi da ɓangaren tattalin arziƙi ba, domin tattalin arziƙin ƙasa na cikin mummunan yanayi, kowane ɗan Nijeriya na kokawa”
Obasanjon ya ƙara da cewar,  “Ba za ka ce don kana yaƙi da Boko Haram shi ke nan ba za ka kula da wannan ɓangare na rayuwar illahin jama’ar ƙasa ba. Dole mu san cewa galibi, matsalar  tayar da ƙayar baya ta taso ne saboda an yi watsi da wannan yanki ta fuskar ci gaba”.
A cikin makon dai kwatsam kamar abin an shirya ne, sai mu ka wayi gari da kwatankwacin wancan bayani daga bakin ɗaya daga cikin na hannun daman shugaba Buhari kuma tsohon mataimakinsa a takarar shugaban ƙasa a tutar jam’iyyar su ta CPC wato Fasto Tunde Bakare. Bakare, ya ce gwamnatin shugaban ƙasar ta jefa Najeriya a halin ci baya maimakon ci gaba.
Mista Bakare ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da huɗuba a Cocinsa da ke birnin Lagos.
A cewarsa, “Wannan gwamnatin ta kafu ne a jigo uku, waɗanda suka haɗa da magance matsalar tsaro da samar da ayyuka da yaƙi da cin hanci, amma idan ka duba babu abin da za ka gani sai alamomin taɓarɓarewa”.
“Tsakanin shekarar 2015 da 2017, adadin matasa marasa aiki ya tashi daga mutum miliyan shida zuwa miliyan 16.”
Malamin addinin Kiristan ya ƙara da cewa a ɓangaren yaƙi da cin hanci, wanda ake ganin ke da muhimmanci, gwamnati ta gaza. Kuma ya ce ‘Buhari ne ya jefa Najeriya a yunwa da talauci’
Ya kara da cewa babu abin da ya daɗa tabbatar da gazawar gwamnatin Shugaba Buhari kamar rashin iya magance matsalar tsaro.
Alh. Ghali Umar Na-Abba tsohon kakakin majalisar tarayya ne a jam’yyar PDP,  shi ma dab da shiga kakar zaɓe ta 2015, ya runtuma tsalle ɗaya ya fada jam’iyyar ta  APC. shi ma cikin makon jiya ya murza giyar baya inda ya bayyana shugaba Buhari a matsayin wanda ya ke mulki irin na mutum ɗaya. Ya kuma yi tofin-ala-tsine ga shugabancin Mallam Muhammadu Buhari.
Kamar yadda Jaridar Daily Trust ta wallafa ya ƙara da cewa: ” A shekaru uku da ya yi a mulki, sam Shugaba Buhari baya aiki da jam’iyya, ya kuma ɗauki ƴan jam’iyya a matsayin maƙiya. Baya shawara da kowa daga ƴan jam’iyya. Ni din nan ɗan majalisar zartarwa ne na jam’iyya duk da dai a jam’iyyance ba mu komai”.
A karshe Ghali Umar Na-Abba ya nisanta kansa a kiran wai Buhari ya zarce ga Shugabancin ƙasar nan.
Uwa kuma Uba ga jam’iyyar waliyyan wato Cif Bisi Akande, wanda shi ne tsohon shugaban riƙo na APC. kuma su ne su ka yi uwa suka yi maƙarbiya ganin Buharin ya ɗare kan kujerar mulkin ƙasar. Shi ma ya ce Najeriya ƙarƙashin shugabancin Buhari tana aiwatar da tsarin dimokraɗiyyar sojoji ne kawai. Wannan tsegumi nasa ya jawo cece-kuce tsakanin magoya bayan jam’iyyar wanda suke ganin wani bita da ƙulli ne a fagen siyasa.
Tirƙashi, waɗannan daman maganganu ne da masana tattalin arziki da masu sharhi akan al’amuran yau da kullum su ke ta nanatawa ba dare ba rana. Tun farkon kamun ludayin wannan gwamnati dai ake ta yi mata hannunka mai sanda, domin dai ankarar da ita ko ta canja yadda ta ke watangaririya da sha’anin tattalin arzikin ƙasar nan. Masanan sun fada cikin sirri da bayyane a bangarori da dama, kama daga tashin farashin dala, tsadar kayan masarufi, rashin biyan ma’aikata hakkinsu na watanni, rashin kulawa da bukatun kamfanoni, rashin samar da wadatacciyar wutar lantarki, rashin cikakken tsaro. Balle uwa-uba aiwatar da manyan ayyuka a duk faɗin ƙasar. Wanda SAKACI shi ya assasa ƙaruwar talauci a duk faɗin ƙasar tun daga hawan wannan gwamnati.
Lallai matuƙar aka bar wannan tawaga ta ƴan ‘bani-na-iya’ ta zarce to talakan Najeriya zai ƙara faɗawa aya zakinta.

LEAVE A REPLY