Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
Daga Ado Abdulahi
Rudani irin na siyasa ya mamaye jagoran kwankwasiyya na kasa Dr Rabi’u Musa Kwankwaso a daidai lokacin da ake shirin shiga kakar zabe mai zuwa. Tsohon gwamnan na jihar Kano, sau biyu a tutar jam’iyyar PDP (1999-2003 ) da kuma (2011-2015) yana mulkar jihar. A zangon sa na karshe ne ya juyawa jam’iyyarsa baya ya canja sheka zuwa jam’iyyar adawa ta APC inda ya yi yunkurin samun takarar shugaban kasa, amma shugaban kasa mai ci ya kayar da shi inda ya sami matsayi na biyu. Mataimakinsa Dr Abdullahi Umar Ganduje shi ne ya dare mukamin gwamna a jam’iyyar ta APC wanda yanzu shi ne jagoranta a jihar ta Kano.
Kwankwaso ya shiga tsaka mai wuya inda al’umara a halin yanzu sun rincabe masa ya rasa gaba zai yi ko baya domin ita dai helikwatar jam’iyyar APC daga Habuja ta nuna ba ta yi da shi inda ta zuba masa kasa a fuska wajen tsige shugaban jam’iyyar na Kano wanda yana bangaren kwankwasiyya ne, ta maye gurbinsa da wanda zai yi biyyya ga bangaren gwamna Ganduje. Kenan Kwankwaso a jam’iyyar APC ko shi ko wani mai goya masa baya bashi da hurumin tsayawa takarar kowane mukami kenan a zabukan 2019. Domin kamar yadda yar manuniya ta nuna hatta zaben kananan hukumomi da za a yi a watan Fabrairu mai zuwa duk yan takarar Gandujiyya ne babu bangaren kwankwasiyya ko daya. A takaice dai kwankwaso a APC BA SHI GA TSUNTSU BA SHI GA TARKO. Babu kima a APC ta Habuja babu tagomashi a APCn Kano.
Alamu a halin yanzu suna nuni babu abin da ya ragewa Jagoran kwankwasiyyar illa ficewa daga jam’iyyar APC shi da dimbin magoya bayansa domin samun madogara da dorewar  tafiyar siyasarsa. Wasu suna rade radin ungulu za ta koma gidanta na tsamiya wato ya koma jam’iyyarsa ta PDP. Sai dai inda gizo ke sakar shi ne, a halin yanzu jam’iyyar tana hannun wanda masana al’umaran siyasar jihar su ke ganin abokin hamayyarsa ne wato Malam Ibrahim Shekarau wanda a halin da are ciki yanzu ya riga ya kame jam’iyyar tamau,  inda matukar kwankwaso ya yi tsautsayin komawa to zai kwashi kashinsa a hannu domin ba za su ba shi fuska ko wata kafa da zai tsaya ko ya tsayar da wasu yan takara a zaben 2019 mai zuwa ba.
Sai dai wani hanzari ba gudu ba,  wasu masana suna ganin abu mafi sauki shi ne kwankwaso ya yi kunar bakin wake ya afka jam’iyyar nan ta PRP wacce har yanzu tana da saukin tallatawa ga jama’ar Kano domin farin jinin Jagoranta na farko wato Marigayi Malam Aminu Kano.
Wasu kuwa suna da sabanin ra’ayi inda suke ganin me zai hana ya yi kukan kura ya shiga sabuwar jam’iyyar nan wato  DPN mai alamar hannu?
To shin mun iya cewa abin da gwamna Ganduje ya ke nufi ya tabbata kenan inda ya ce sun yiwa kwankwasawa KURUN-KUS a siyasar Kano?  Ma’ana siyasar kwankwaso ta zo karshe ?
Lokaci ne kawai zai iya tabbatar da  haka.
Domin dorewar darikar ta kwankwasiyya a  siyasar Kano, dole ne jagoran ya zurfafa tunani kafin yanke wannan hukunci mai tsada, yana kuma bukatar shawarwari daga masoya da abokan arziki a fagen siyasa a waje da cikin jihar Kano.

LEAVE A REPLY