Da matan da suka zabi bariki da biyewa maza wajan cin lokaci da shekewa bisa tunanin cewa lokacinsu ne suke ja zasuyi duba tare da daukar darasi daga masana’antar kannywood lallai inaga da yawa zasu hankalta su koma cikin hayyacinsu.
Yi duba kawai zuwaga Ali Nuhu, Sani Danja, Sharif Momo ka tuna yadda har yanzu wadannan mutanen suke jan zarensu a duniyar finafinan hausa inda mukan iya ambatansu da jigogin tafiyar na asali a farkon lokaci, wadanda akayi yayinsu shekaru da dama da suka wuce kuma har yanzu suna cin duniyarsu da tsinke a masana’antar ta film.
Ka dawo cikin zuciyarka ka tuna Fatee Muhammad, Saima Muhammad, Hafsat Shehu da abunda yayi kama dasu. Sunanan fa da ransu ba mutuwa sukayi ba, amma an daina yayinsu ba tare da sun rasa komai cikin jini ko jikinsu ba, kawai dai zamanine yabi dasu ake ganin akwai bukatar gabatarma da duniya sababbin fuska wadanda suke da danyan jini tare da abubuwan so da burgewa ga mutane.
Wannan Itace Rayuwar
Mata sauda yawa sunama kansu kallon wani dogon lokaci da damagaresu ba suci zamani ko lokacinsu a tsakananin gidan iyaye makaranta da gidan kawaye, yayin da zuwa biki da hawa motar samari da abokai ya zame masu abun alfahari ga wadanda mutar take matsala ko abun burgewa garesu, ta bangare guda kuma kaga matanne ke bibiyar mazan da basu abun alatun duniya saboda burgewa da kokarin ganin sun sami damar biyawa kawunansu bukata a lokacin da suka ware suke tunanin nasune na hutawa da holewar rayuwarsu.
Ki Sani Yar’uwata
Hakika martaba da darajarki itace tsare kanki da mutuncinki daga biyewa zamani domin neman abun duniya ko wata shahara da kike tunanin nema ko hange a wannan duniyar.
Abun takaici zai koma maki a duk lokacin da kika wayi gari Ki Naji Kina Gani Duniya Ta Ajiyeki Ta Dauki Wasu Sababbin Jini wadanda kilama kin fisu asali, kira, diri, kyau, ilimi, kwarjini da abun duniya. A haka kina kallo wanda a baya yake furta maki cewa baya da kamarki ko kike ganin babu abunda zai iya ba tare dake ba zakiji koma ki gani da idanuwanki yana shagali da bushasharsa cikin walwala da annashuwa da wasu danyen jinin ke ya wuce da sani hadi da zamaninki.
Wata kagaggiyar kissa da take kayatad dani dana taba karantawa a shafin zada zumunta mai dauke da darasi na hankali da luratarwa ga matan yau. ” Wata matace ta lura da halin da yarta ta shiga na bibiyar maza dakokarin neman tara abun duniya da harkar holewa, sai wannan matar ta kira yarta ta zaunar da ita ta bata hotunanta guda biyu daya tun tana budurwa dayan kuma ba’a dade da dauka ba, tace mata kalli hotunannan biyu da kyau in kin lura duka nice, kalli kirjina da yadda nake lokacin ina kamarki amma kalli yadda na koma yanzu. Nimafa kenan babankine kawai ya tasani gaba na koma haka, yaya kike gani da hangen idan da mazane nakebi kamar yadda kikeyi yanzu? Uwar ta amsama yar da cewa wallahi da na ninka haka lalacewa nesa ba kusa ba, saboda haka kiyiwa kanki fada”.
Hakika ga duk mace mai hankali ya kamata ta koma cikin hayyacinta a lokacin data taso taga tsararrakin mamanta maza da yadda suke kamar ba tare sukayi yarinta ba.
Wani Abun Tsoro
Kinama lalacewar da shagalar ba tare da hararo me zai iya zuwa ya komo ba, yaushene mutuwa zata riskeni, a wane haline mutuwa zata iya samuna, wane tabbaci gareni cewa zan kai gobe. Kaje nema bayani a kan layin su yarinya maimakon kaga ana wahala wajan fadan wata illa ko damuwa a gareta, sai dai kaga ana kame kamen gano alhairai da ingancinta.
Mata da aka sani da kunya hadi da kawaici, sune suka wayi gari suke ake samu da roke roken abun duniya da raka maza unguwa tare da fita gida lokacin da zuka zaba su kuma dawo lokacin da sukaga dama. Kaga mace bata dauki nuna tsiraici ko bayyanashi a bakin komai ba akan wani abu da batama da tabbacin samunshi gareta, wata jikinta gaba daya zata bayar kila saboda hasashen samun wani abun ko kuma kawai saboda biyama kai bukata.
A haka kuma kullum iyayen kallon yara suke masu wadanda basuma san inda duniyar shagala da holewa ta dosa ba, ko kuma kaji suna cewa aini tabbaci da ingancin da nake dashi akan wance na tabbata ba zatayi wani abu daya saba ba a duk inda take.
Mu Koma Kannywood
Kuyi duba zuwaga wadancan mazace da muka ambata wadanda har yanzu a film sukan iya fitowa a samari wadanda basuyi auren fariba yayin da ku kuwa iya gatan da za’ayi maku shine ku fito a zawarawa ko kuwa matan gida, wani lokaci ku fito a matan iyayensu koma ku amsa sunan iyayen nasu mata duk kuwa da tabbacin da kuke dashi cewa a shekaru kun girme masu
Waiwayo kan irinsu Jamila Nagudu, Aisha Tsamiya, Hadiza Gabon meye suka rasa meye basu dashi meye mace zata nuna masu? Amma banan gizo yake sakarba sun riga sun zama tsohon yayi sai dai su fito a auren latti amma ba’a yammata gangariya ba.
Yi duba zuwaga yaran dasu Ali Nuhu, Sani Danja, Adam Zango da ire irensu suke shiri dasu a yau kananan yarane fa da dukan wadancan dana ambata sun haifesu imma basu da wadanda suka fisu.
Hakafa abun yake a ko ina bawai a Kannywood kawai ba, a ko ina kika leka zaki tarar da hakan. Wanda kika biyewa wajan lalacewa ana samun sabon jini amsarshi zatayi saboda haka tsarin yake, ke kuma a lokacin gani yakeyi kinyi masa tsufa jikinki da duk wani abu da yake bukata yanzu Ready Made yakeso ba wanda yaga jiya yaga yau ba.
Yar’uwa Kiyi Nazari
A gidan aurema da ake yawancin abubuwa bisa tsari da ka’ida na shari’ah zaki samu maigida ya auro yarinya tsarar yar cikinsa tana gogayya da sauran matansa a matsayin matar aure bai zama abun magana bare Allah wadai a duniya ba. Amma ke kuwa dakin aurei yaro tsaran dan cikinki gulma da maganganu marasa dadi sun dingi bi ta cikin kunnuwanki kenan duk kuwa da cewa babu inda shari’ah ta hana hakan.
Abun Akwai Tashin Hankali
A wayi gari mutum ya mutu ka zauna ka kasa tuna wani aikin alhairi daka sani tsakaninsa da mahaliccinsa wanda kake tsammanin Allah ya duba ya rangwamnata masa, duk kuwa da cewa ba’a shiga tsakanin Allah da bawansa, amma ai inaga zaifi zama alhairi ace bawa ya tanadi wani guzuri da zai amfaneshi gaban Allah idan an hadu.
Jan Hankali Garemu
Hakika wannan duniyar fararriyace kuma kararriya, kuma duk abunda mutum yake aikatawa Allah yana kallonsa kuma zaiyi masa sakamako akan dukkan abunda ya aikata.
Bamu da wani tabbaci akan yau din da muke ganin mun riska, bare kuma goben da bamusan meta kunsa ba. Kowane minti na iya zama lokacimmu na karshe a cikin wannan duniyar, kowace rana na iya zama ranarmu ta karshe a wannan duniyar, kowane aiki na iya zama aikimmu na karshe a cikin wannan duniyar. Bamu da wani isasshen lokacin holewa ko cin duniya da tsinke.
Natsu sosai yar’uwa nasan zaki karu sosai daga darussan da suke kunshe cikin wadannan hotuna da suke kasan wannan rubutu da nake tunanin idan muka karantashi da budaddiyar zuciya zai amfanemu baki daya
Mu Sani, Allah yananan yana jiran kowanemmu a madakata, zai kuma yi mana sakamako dai dai da yadda muka aikata ko muke aikatawa
Allah Ka Bamu Dacewa Ka Shiryemu Baki Daya.

LEAVE A REPLY