Hassan Abdulmalik

Wato babu rashin kimanta dan adam sama da hukuncin da shugaba Muhammadu Buhari ya yanke na ya zabi halartar bikin aure sama da ziyarar jihohin kasar nan da a baya-baya nan suka fuskanci tsananin tashin hankali sakamakon ibtila’in da ya same su. Misalin wuraren sun hada da: Dapchi, a jihar Yobe, Mambila, a Taraba, Binuwai, Zamfara da dai sauransu.

Zabin na shugaba Muhammadu Buhari na ya halarcin daurin auren ‘yar gwamnan Kano, a Kano, ya sake dawo min da tambayar nan: Shin shugaban na da mashawarta ma kuwa ?

A wani lokaci a baya, ‘yan Nijeriya sun koka cewa shugaba Buhari bashi da mashawarci a kan harkokin siyasa, sai shugaban ya yi hobbasa ya zabi Sanata Babafemi Ojudu, amma kuma sai ya tura shi ya yi aiki a ofishin mataimakin shugaban kasa. Wannan shawara ta shugaba Buhari na ya tura mai bashi shawara kan harkokin siyasa ya koma ofishin mataimakin shugaban kasa da aiki, ta sanya ni ina ta maimata fadin ‘Ikon Allah sai kallo,’ a cikin zuciyata.

Ga duk wadanda ke ganin cewa shugaban kasa ba shi da bukatar mashawarci kan harkokin siyasa, ina mai farin cikin sanar da shi cewa, tsarin mulki irin na Buhari, da ‘yan uwa da abokan arziki suka zamto sune masu ruwa da tsaki, tafiye-tafiye zuwa kasashen waje babu ji babu gani, mayar da hankalin a kan yankin arewa sama da sauran yankunan kasar nan, tare da tafiyar wahainiyar da gwamnatin Buharin ke yi alamu ne da ke nuna muhimmanci ofishin mashawarci ga shuganban kasa kan harkokin siyasa.

Haka kuma dai, a lokacin da muka matsawa shugaba Buhari lamba da ya nada kwamitin tattalin arziki, a lokacin kasar na cikin matsin tattalin arziki, sai Buhari ya sake amsa kiranmu, ya nada Dakta Adeyemi Dipeolu, a wannan karin ma dai, ya tura shi ofishin mataimakin shugaban kasa. Ni dai kam ban taba ganin shugaban da bashi da kishin tattalin arzikin kasar da ya ke shugabanta ba irin Buhari!

Ni a gani na, ba wai kawai barin mashawartan biyu (na siyasa da na tattalin arziki) shugaba Buhari ya kamata ya yi a ofishinsa ba, a’a! Kamata ya yi a ce suna tare da shi a kowane motsi don su ne za su yi wa gwamnatinsa saiti na siyasa da tattalin arziki. Abin yana daure min kai yadda shugaban kasa ya ke ganin cewa bashi da bukatar karbar shawarwarin mashawartan biyu kai tsaye daga bakinsu.

Daga abubuwan da ke wakana a kasar nan, za ka fahimci cewa shugaba Buhari ya fi damuwa da masu rike da madafun iko sama da talakawa. Ga kuma duk wanda ke da wancan tunani na cewa shugaba Buhari na da kishin talaka a ransa, to, ya ma ajiye wancan tunanin!

LEAVE A REPLY