Ahmad Sabo

Duk da a wajen wasu hakan zai iya zama banbaraqwai, amma hakan ba zai hanani bayyana abinda na fi gamsuwa da shi ba. A wajena saboda wasu qwararan dalalai na fi son uwar jam’iyyar PDP ta sahallewa kwankwaso wakiltarta a kakar zabe ta 2015.

Dalilaina

1- na gamsu cewa tuqin hannu daya Shugaba Buhari yake yi was qasar nan, wanda hakan ya munana kowanne bangare na turakun cigaban qasar nan. Ni kuma a ganina irin salahar da Buhari ya rsa akwai ta a wajen kwankwaso, wato bibiyar ayyuka, kulawa yadda yakamata kulawa da muradun talakwa, qarfafa ilimi da dawo da martabar aikin gwamnati, gina qananan masana’antu ta hanyar bayar da jari.

2- Kano it a CE cibiyar siyasar Buhari kuma quri’n jihar Kano kadai ka iya sabbaba faduwar Buharin, sannan kwankwaso dan jihar Kano ne, kuma tabbas dondazon kanawa za su yi fitar dangi wajen zazzaga wa Rabiu kwankwaso quri’u.

3- a Arewa kaf! A yanzu babu wani dan siysa mai tarin Nagoya baya Lamar Rabiu kwankwaso, wanda ina da yaqinin zai Iya bayar da ruwa ga Shugaba Buhari a babban zabe.

Idan muka kalli qididdigar masu kada quri’u dole mu kalli yankuna zabe guda shida (six geo political zones) da irin rawar da suke takawa wajen kada quri’a, bari mu fara da Arewa. dama Arewa maso gabas ta Buhari ce, idan har an bawa Kwankwaso takara Arewa mask yamma za a raba quri’unsu ne. Sannan Arewa ta tsakiya tsautsayi ne ya za suka yi APC, a yanzu alamu na nuna cewa PDPnsu za su koma. Kudu maso yamma basu da tabbas, amma zama kowa ya san halin Bayarabe, ko a addini sai ya raba qafa ballantana a siyasa, wadannan su dama raba quri’unsu za su yi.
Sai Kudu maso gabas PDP sak! Kudu maso maso kudu suma PDP sak!.

Ya Allah ka ba wa Kwankwaso qasar nan, kuma ka qarfafe shi da qarfinka da buyarka ya Allah

LEAVE A REPLY