Sheikh Ahmad Gumi
Daga Abu Hanifa Dadiyata
A cikin shekarar 1984 lokacin Muhammadu Buhari yana ‘kololuwar mulkin sa na soja, yana matashi ‘dan kasa da shekaru 40, giyar mulki na diban sa babu wanda ya tsira daga salon mulkin sa na kama-karya. Ga alamun yunwa da fatara sun fara bayyana a fuskokin mutanen Najeriya, komai ya kama wuri daya ya tsaya chak!
Ana cikin irin wannan zaman zullumin ne wannan shaharrarren Shehin Malamin dake garin Kaduna wato Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya fara sukar gwamnatin Buhari da kakkausan murya yana nusasshe ta irin kurakuren da take tafkawa.
A wannan lokacin, Malamai da dama basu gamsu da salon Mulkin Buhari ba amma suna tsoron sharrin Soja. Saboda cikin dare daya sai su hallaka mutum cikin ruwan sanyi, amma kasancewar Mallam Gumi Jarimi, mara tsoro mai fayyace gaskiya komai ‘dacin ta, ya ci gaba da sukar Gwamnatin Buhari har ta kai ga Buharin ya fara mayar da martini a wurin wani taro yace “ya kamata malamai su daina tsoma baki a cikin harkar siyaysa”. Wannan martini bai sa Gumi ya tsagaita wuta ba, hasali ma hakan kara masa kwarin gwiwa yayi wurin ci gaba da sukar gwamnatin Buhari musamman yadda yake kama mutane yana daurewa ba tare da kwararan dalilai ba.
Ana cikin haka ne wata rana jami’an tsaro na fararen kaya suka zo har gida suka yi awon gaba da Mallam Gumi ba su tsaya ko ina ba sai a garin ikko (babban birnin tarayya a wancan lokacin). A lokacin gwamnatin Buhari ta kwace paspo din Mallam, sannan yana hannun hukuma a ikko har watan Ramadanan shekarar ta shigo, ga tafsiri za a fara a masallacin sa dake sultan Bello amma ba a sako shi ba, hakan ne silan fara tafsirin Mallam Lawal Abubakar wanda ya haye kujerar ya maye gurbin mallam gumi kafin gwamnati ta sako shi.
Amma duk da irin wannan dambarwa da kai ruwa rana da aka yi tsakanin Marigayi Mallam Abubakar Gumi da Buhari sai gashi wasu ‘yan bana bakwai, malalata wadan da basu karanci tarihi ba sun fito suna sukar Dr Ahmad Gumi dan ya soki Buhari kuma suna yabon Sheikh Abubakar Gumi wai shi ba ruwan sa. Dama an ce rashin sani ya fi dare duhu, da ace sun san yadda aka sa zare tsakanin marigayi Mallam Abubakar Gumi da Buhari wallahi da basu fadi haka ba.
Sukar da Dr Ahmad yake yiwa Buhari ya ‘kara tabbatar min da cewa Dakta ‘dan halak ne, dama an ce kyan ‘da ya gaji uban sa. Ya gaji fadin gaskiya wurin mahaifin sa, dan haka ya cancanci yabo. A dai dai lokacin da mafiya yawan malaman addini mulunci da ke arewa sun mayar da kawunan su ‘yan amshin shata, ‘yan a bi yarima a sha kida, sai pantamawa suke suna wadaka cikin daloli, suna hawa motoci na alfahari, suna sanya kayan ‘kawa alhali mabiyan su na cikin zunzurutun yunwa, talauci da
 patara, sannan duk wanda ya nemi ya soki salon mulkin Buhari sai su yi ta masa luguden ayoyi da hadisai, ko su ce mutum ya zama fasiki.
Bayyanar Dakta Ahmad Gumi a dai dai wannan lokaci da ‘yan arewa da dama idanun su ya rufe alheri ne a gare mu. Da fatan Allah ya kare Dakta daga sharrin masu sharri, ya kuma ‘kara azurta mu da malamai masu iya fadawa gwamnati gaskiya komai dacinta.

LEAVE A REPLY