Daga Baba Bala Katsina
Ko da Buhari ya cika kowane irin alkawari daya dauka, baza fa mu ga irin cigaban da muke tunani ba, ma damar kawai abunda da GWAMNONIN MU SUKE YI KUMA MUKE SON SU AKAI SHINE SUNA (JAM’IYAR BUHARI)  “SON BUHARI”. Duk kokarin da Buhari zai yi a bangaren ilimi, kiyon lafiya da sauran su, a salansa zamu ji fa!, in dai bamu sa ido wurin ganin gwamnatocin jahohin mu sun mai da hankali akan wadannan bangarorin ba.
Yi tunani mana: gwamnatin tarayya ta shigo da tsarin fansho da take ganin zai taimaki ma’aikata, amma dayawa daga cikin jahohi sun kasa shiga irin wannan tsarin. FG ta yi tsarin asusun bai daya (TSA), ta kirkiro da hanyoyin yaki da rashawa da cin hanci irin su EFCC, ta shigo da tsarin kiwon lafiya na bai daya da sauran su, amma dayawan jahohi, sun kauda kai, sun yi kiri da muzu. Har yanzu, duk wadannan kokarin da FG data yi bai sa muka samu saukin rayuwa ba. Anan arewa ma abun sai ya ta’azzara.
Mu kula sosai, duk jahar data ci gaba, ba taci gaba bane kawai dan gwamnan ta na son shugaban kasa ko kuma dan ta dogara da ayyukan da FG zata yi, a’a, jahar taci gaba ne dan tana inganta harkokin gudanar da mulki da tsatsare na jahar ne. Arzikin Kasa, tsare-tsare na gudanarwa wanda ke leading to cigaba are always local. Look inwards, strength din mu na nan.
Abunda FG ke kawowa fa makamashi ne na cigaba idan jaha tayi abunda ya dace. Shiyasa jahar Iko zata ce FG tayi mata wani titi ko hanyar ruwa ko jirgin kasa dan inganta kasuwar data inganta kuma ta samar ma tsari mai kyau. Gashi yanzu ita ke koya ma FG tsari da gudanarwa, Kuma tsofaffin ma’aikatan ta ke fidda Buhari kunya saboda sun yi aiki a tsari mai inganci in Nigerian context. Buhari ya tabbatar da haka daya je bude tashar jigila ta motocin sufuri a jahar.
Kawai dan gwamnan mu na jam’iyar Buhari kuma yana cewa yana “goyon bayan Buhari”, Ba fa shi zai kawo mana ci gaba ba ko da shi Buharin ya yi rawar gani a bangarorin inganta rayuwa.
Da dai zamu maida hankali akan abunda ake a jahohin mu kuma mu tilasta ma GWAMNONIN mu da su yi abunda ya dace, daya fi mana, saboda CIGABAN MU BAYA ABUJA.

LEAVE A REPLY