Daga Daliban Kano a Sudan

Amadadin daliban Gwamnatin jahar Kano da gwamnati ta dauki nauyin karatun su a kasar Sudan dake karatun likitanci, muna amfani da wannan dama domin tunatar da mai Girma Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, dangane da rashin biyan kudaden abinci kimanin watanni sama da 20, kudaden gida na shekarar karatu guda da ta wuce da wanda za,a shiga da sauran abubuwan da suka wajabta cikin karatun mu.

Mai Girma Gwamna, kasancewar mun kammala shekarar karatu cikakkiya ba tare da karbar ko sisin kobo ba na tallafi daga Gwamnati wanda hakan yayi sanadiyar shigar mu cikin mawuyacin hali. An kai ga yanayin da abincin da zamu ci ma wahala yake mana ga kuma takura da muke samu daga masu gidajen da muke haya wanda a ko da yaushe barazanar korar mu suke yi matuqara bamu biya su kudaden su ba.

A halin da ake ciki akwai dalibai mata da suka kammala karatun su amma sun kasa karbar takardar shaidar kammala karatun sannan kuma masu gidajen da suke ciki sun kwace musu fasfo (international passports) kasancewar basu biyasu kudin su na shekarar karatu cikakkiyya. Wanda hakan yasa baza su iya dawowa gida ba.

Bugu da kari, akwai dalibai a Jami’ar Alrazi wanda zasu fara shekarar karatun su na karshe wanda idan basu biya kudin makaranta ba baza’a bar su su shiga aji ba wanda a karshe hakan zai sa a hana su yin jarrabawar kammala karatun su.

Daga karshe, muna nuna yabawar mu da dukkan kokarin da wannan Gwamnati takeyi na ganin mun kammala karatun mu kuma muna fatan mai Girma Gwamna zai ji kukan mu domin kawo mana dauki daga mawuyacin halin da muke ciki.

Wassalam,
Daliban Jihar Kano da Gwamnati ta dauki nauyin karatun su a Sudan.

LEAVE A REPLY