Mansur Ahmed
Mansur Ahmed
Shure – shure baya hana mutuwa inji Hausawa kuma gudun kaddara shine guzurin tarar da ita, kamar yadda fir’auna bai hana kaddarar annabta ta Annabi Musa ba, haka bana ganin akwai ikon Allahn da zai hana kaddarar da Allah ya rubuta faruwarta akan Sule Lamido da iyalinsa.
1. Takardar Farko
31- January, 2016
Dakatarwa Daga aikin Hakimi a gundumar Bamaina da Kiyawa Bisa Umarnin Gwamnatin Jigawa
Bisa Umarnin da mai martaba Sarki ya samu daga ofishin sakataren Gwamnatin jihar Jigawa mai Lamba SSG/AF/S/A/14/VOL.III/82, Ranar 29 January, 2016.
2. Takarda ta biyu
Takardar neman k’arin bayani
Takardar da majalisar Sarkin Dutse ta samu daga karamar hukumar birnin kudu mai lamba BKLG/PDM/ADM/26/VOL.1/658 Ranar 12/4/2018 da Karamar hukumar Kiyawa tana neman Karin bayani game da shigar San Turaki harkokin siyasa duk da cewar an dakatar dashi daga sarauta kimanin shekaru 2
3. Takarda ta uku.
Amsar takardar neman Karin bayani
Ina mai tunatarwa cewar ni yanzu bana matsayin hakimi mai kasa tun bayan dakatar dani da fadar Sarki tayi bisa umarnin Gwamnatin Jihar Jigawa ta karkashin sakataren Gwamnatin Jigawa, duk.da haka karamar hukumar birnin kudu tana bibiyar mu’amulolina a matsayin dakataccen hakimi mai kasa wadda nake tunanin bata da wannan hurumin, shekara biyu bana shiga harkokin fada saboda an dakatar dani  har ma an turo wakili yana gudanar da harkokin kasa ta, a Matsayina na Dan Nigeria doka ta bani dama nayi mu’amula da kowa matukar ban karya tsarin mulki mulkin Nigeria ba dogaro da Sashi na 40 na kundin tsarin mulki Najeriya
4. Takarda ta hudu
Ranar 30 – 04 – 2018.
An karb’i gundumar masarautar Bamaina daga wajen Mustapha Sule Lamido da gundumar Kiyawa daga Hannun Aminu Wada Abubakar Kiyawa kuma majalisa ta yarda a tura sabon hakimi ya cigaba da hakimcin gundumar Bamaina da gundumar Kiyawa
A lokacin da ake kokarin hana Allah yayi Ikonsa watakila kaddarar karbar mulkin Badaru San Turaki da Dokaji shine silarta, domin dakatar dasu a hakimi da aka yi a baya shine sanadi samun karbuwarsu a wajen jama’a, na tabbata kwace gundumar a wajensa duk da cewar gadonta yayi zai sake samun wata daukakar da karfin Ikon Allah.

LEAVE A REPLY