Malam Abdullahi Abubakar Dean, me sharhi kan sha'anin tattalin arziki da Falsafa
Shi tsarin jari-hujja a durƙusassun kasashe irin namu ya zama tamkar sandar fito ga manyan ƙasashe.
Ɗan kwadago a kasashenmu zai kasance ya kai shekara talatin ko sama da haka yana aikatau ba tare da ya fahimci cewa gina wasu kawai yake yi ba.
Tsari ne za mu iya masa kallon na ruwa mai fansar ko ceton (bailout) na tudu.
Abin nufi a nan shi ne; manyan kasashe inda tsarin jari-hujja ya kai matsayin fidda-gemu, ba zai taba ɗorewa ba in ba tallafi ko ceto na zuwa gare shi daga gumin durƙusassun kasashe ba.
Tazarar da muke gani wajen darajar naira (guminmu) in aka kwatanta ta da kuɗaɗen ƙetare shi ke haska mana irin tallafin (bailout) da muke bai wa manyan duniyar, da ma karnukansu da ke fake a cikinmu.
Hikimar siyasar tattalin arzikin musayar kuɗi (political economy of exchange rate) ke nan. Haka ake ta mirginawa muna k’ara nisa amma ƙura kawai muke shaƙa
Muddin hakan ya dawwama to tamkar bauta wa tsirarun cikinmu muke yi a hannu guda, muna kuma bauta wa wadancan kasashe a daya hannun.
Zaizayar darajar naira a fakaice abin da yake haskaka mana ke nan. Dangane da ƙarin albashi, tayar mota ake ba mu cike da iska muna murna, sai mun hau titi (mun isa kasuwa sayayya) sai mu ga ashe a sace take.
Muna komawa gida sai mu gane ashe tuni an yashe mu tatas. An amshe ƙarin, dama wani sashin na gangar jikin.
Tsawon wadannan shekaru na bauta (ƙwadago) haka abin yake; fafalolo ne kawai. Kuma shi ne sirrin habakar tattalin arziki (economic growth) da kullum ake ta mana ihu a kai.
An ce ma ka fi kowace kasa arziki a Afirika, amma a zahirance sai ka gan ka kullum jiya-i-yau, koma in ce gaba ta fi baya lalacewa, a inda a daya hannun kuma wasu tsiraru ne ke kara fantamawa suna tashi (cikin private jets) a sama kamar tsuntsaye, daga wannan tsibiri zuwa wancan a cikin duniyar da guminka ne ya gina ta, kuma ya yi mata ado.
Wannan shi ne a takaice murɗi (dialectics) na musayar kudi da tazarar da ke tsakani kuɗaɗen.
*Wannan irin rubutun ke kara nuna mani cewa za mu iya koyar da duk wani fannin ilimi cikin harshen Hausa kamar yadda marigayi Dr Bala Usman ya koya mana tun a shekarar 1985.

LEAVE A REPLY