Daga Dr Aliyu Muh’d Sani

Su Musulmai masu imani sun yi imani da Allah da Ranar Lahira, kuma sun yi imani da Manzon Allah da abin da aka saukar masa na Alkur’ani da Sunna. Wannan ya sa suke da’a wa Manzon Allah (saw) suke bin umurninsa suke aiki da maganarsa a cikin ingantattun Hadisansa, saboda Allah ya ce:

“Ba mu aiko wani manzo ba sai don a yi masa da’a bisa izni da umurnin Allah”.

Saboda haka sun san cewa; hakikanin imani da Manzon Allah (saw) shi ne yi masa da’a da biyayya a komai.

Kuma hatta hukunci da suke yi a shugabanci da alkalancinsu duka suna yin aiki da hukuncin Allah da Manzonsa (saw), ba sa jefar da duk wani hukunci da Annabi (saw) ya yi a halin rayuwa gaba daya, saboda sun san cewa; imani na gaskiya shi ne aiki da hukuncin Allah da Manzonsa a kan komai kamar yadda Allah ya ce:

“Na rantse da Ubangijinka, ba za su yi imani ba face sun sanya ka matsayin mai hukunci a dukkan abin da ya faru na husuma a tsakaninsu, sa’annan kuma ba za su ji wata damuwa a zuciyarsu a kan hukuncin da ka yi ba, kuma su mika wuya matukar mikawa”.

Amma su kuma Zindikai ‘Yan Boko Aqeeda fa, su ne dai Munafukan da suke raya sun yi imani da Allah, sun yi imani da Annabi, sun yi imani da Alkur’ani, amma da zaran an ce; to ku yi aiki da Alkur’ani da Hadisan Annabi (saw) a ibada da halin rayuwarku na siyasa da alkalancinku sai su ki, su zabi aiki da wanin abin da Allah ya saukar. Kamar yadda Allah ya ce:

“Shin ba ka ga wadanda suke raya sun yi imani da abin da aka saukar gare ka da wanda aka saukar kafinka ba, amma kuma suna son kai hukunci zuwa ga Dagutu, alhali an umurce su da su kafirce masa, amma Shaidan ne yake so ya batar da su bata mai nisa”.

Saboda haka da zaran ka ga mutum Musulmi yana raya ya yi imani da Allah da Annabi da Alkur’ani, amma kuma yake ganin aiki da Shari’ar Muslunci cibaya ne, ko rashin wayewa ne, ko bai dace da wannan zamani ba, ko akwai takurawa a cikinsa, ko a kwai danne hakkin bil’adama, ko akwai hana ‘yancin rayuwa, ko riko da Addini tsattsauran ra’ayi ne, ko yana janyo ra’ayin ta’addanci, da sauran irin wadannan tunani, to yana cikin wadannan Munafukai Zindikan da Allah ya yi magana a kansu a cikin wadannan jerin Ayoyi.

Su kam Muminai Musulmai na gaskiya suna imani da Allah da Manzonsa suna riko da Addininsa, suna aiki da Shari’arsa a cikin dukkan rayuwarsu, suna gaskata Alkur’ani da Hadisan Annabi (saw) kuma suna binsu suna aiki da su a dukkan fagagen rayuwarsu.

LEAVE A REPLY