Yasir Ramadan Gwale, mai sharhi kan al'amuran siyasa a jihar Kano

Daga Yasir Ramadan Gwale

Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, tayi fargar jaj, inda bayan da al’amura suka gama kacamewa ta-dagula tun da jimawa sannan suka magantu kan batun Kwankwaso da Ganduje.

Tun icen wannan rikici yana danye sharaf ya kamata a tankwara shi, amma aka yi shakulatun bangaro da batunsa sai yanzu da 2019 take sake karatowa, ‘yan siyasa masu bukata suka fara shiga hayyacinsu da tunanin ina ce mafita.

A ganina an makara kan wannan batun sasanto da aka wakilta Ahmed Tinubu ya shiga tsakani. Eh, gaskiya an makara, kuma wannan kwamiti na Tinubu babu abinda zai yi sai dai ya sake dagula al’amura, abinda kuwa zai dinga faruwa shi ne barin baya da kura a yayin wannan sasanto.

Ko a jiya an jiyo Gwamnan Kano Ganduje yana cewar su da ‘yan Kwankwasiyya haihata haihata. Wato fau fau fau tsakaninsu. Na saurari kalaman Gwamna naji duk abinda ya fada kan su ‘yan Kwankwasiyya.

Haka kuma, lokacin da aka tambayi Kwankwaso a majalisar dattawa ko yana da abinda zai ce dangane da batun rikicinsa da ganduje yaki cewa komai. Wannan kin magana da Kwankwaso yayi yafi zama abin tsoro ga su ‘yan Gandujiyya, domin da ya yi magana ne za’a san inda ya dosa, amma yanzu ya barsu cikin tararrabi.

A hakikanin Gaskiya, wannan rikici na Kwankwaso da Ganduje ba wai kawai sune ba, kusan ko ina ana fama da wannan rikita rikita a cikin jam’iyyar APC. Gashi nan dai mun gani a Zamfara tsakanin Gwamna Yari da Sanata Marafa da kuma Sanata Yarima a daya bangaren. Haka nan a jihar Oyo tsakanin Gwamna Amosun da Minista Shittu.

Kusan ko ina haka ake fama, kwanakin munga yadda aka tayar da jijiyar wuya tsakanin Gwamna Bello da Sanata Melaye. An yayyafawa abin ruwa, amma kowa yasan tana kasa tana dabo, uwa uba, ga nan jihar Kaduna tsakanin Gwamna el-Rufai da Sanata Shehu Sani, ga Jigawa tsakanin Gwamna Badaru da Sanata Ubali Shitu, a Bauchi tsakanin Gwamna MA da gungun ‘yan majalisar jihar dake Abuja karkashin Dogara duk wadannan jihohi akwai jikakkiya a jam’iyyar APC.

Kai hatta jihar Shugaban kasa ta Katsina,akwai kwantacciya tsakanin Gwamna da su Dakta Bugaje da sauran wadan da suka yi likimo. A Binuwai kuwa kana iya cewar APC ta fadi warwas. Kusan ko ina a jihohin APC haka ake fama da wannan batarnaka. Amma uwar jam’iyya tayi kunne uwar shegu aka ki sauraren kowa.

Yanzu kuma zabe ya kusa, bukatar samun goyon bayan kowanne bangare ta taso a cikin jam’iyya, sannan aka shiga laluben mafita. Wannan ruwan yayyafa masa domin ya lafa tuni ya bushe, su kansu su Tinubu babu abinda zasu yi sai kara dagula al’amura domin a jihohin nan da suke fama da rikicin wasu da dama ba zasu yadda da wannan Kwamitin ba.

Kuma fa batun ba wai iyakar jihohi ya tsaya ba. A saman sama ma akwai shi a kwance, domin akwai gungun ‘yan majalisa karkashin jagorancin Shugaban majalisar dattawa Bukola Sarki, wanda suke yiwa juna kallon hadarin kaji da bangarensu Tinubu, nan ma akwai jikakkiya.

Sau da dama sai ka kasa gane me yasa Shugaban kasa yake jan kafa akan yadda ake ta fama da rikici a cikin jam’iyyar da yake lamba daya, wanda shi yafi kamata ace ya nuna hanyar magance wannan rikita rikita tun da farko.

A baya fa a cikin rusasshiyar jam’iyyar CPC haka aka sha fama da rikici ko ta ina, al’amura duk suka kacamewa jam’iyyar Buhari na gani a lokacin ya kasa yin wani abu, sai daga bisani bayan lamura sun gama cukurkudewa aka ce an nada Nasiru el-Rufai ya zama bakaniken jam’iyyar, shima ya kasa wani katabus haka aka wayi gari CPC ta tsira da jiha daya tal.

To kusan abinda yaci Doma bai cika barin Awe ba. Hada su yake baki daya yayi jana’izarsu, domin yanzun ma bata sake zani ba, irin wancan abu da ya faru a CPC bayan abubuwa sun rikice aka dauko el-Rufai aka bashi kaninakncin jam’iyya, irinsa aka yi yanzu ma,aka dauko Tinubu aka bashi kanikancin jam’iyya, babu kuma wani tasiri da wannan kwamiti na Tinubu zai iya yi.

Wasu zasu dinga tunanin ai babu komai, APC na da Gwamnati, amma sai anzo gab sai kaga komai ya damalmale al’amuran kasa dinkuwa. Ammafa wannan rikita rikita ta APC daman ba wata abin mamaki bace, wanda duk ya kalli yadda aka kunsa abubuwa yasan haka zata faru, mu kam sai dai muce a juri bara wai albasa fara ce tas. Lokaci zai nuna mana ita.

LEAVE A REPLY