Mansur Isa Buhari
Daga Mansur Isa Buhari
Sam ban so tsokaci akan matsalar nan ba. Amma na kasa haƙurin ganin yadda ƴan Arewa ke zubar da mutunci da ƙimar juna akan banbanci ra’ayi.
Maganar gaskiya itace, idan malaman Addini da shugabanni (na gargajiya ko siyasa) za su yi dogon bayani mai aƙalla jimla arba’in akan wata matsala da ta shafi rayuwarmu a matsayinmu na al’umma amma mu watsar da duk abinda suka faɗa a kwandon shara mu mayar da hankali akan kalma ƙwaya ɗaya tak, to za mu shiga cikin ruɗanin da zai iya halaka al’ummar baki ɗaya.
Dukanmu, har mai magana, muna da wannan halin na banhaushi. Misali, lokacin da shugaba Buhari ya yi jawabi akan matasanmu, mun watsar da duk sauran maganar da ya yi mu ka kama kalmar “ci-ma-kwance” saboda ita ce ta yi dai-dai da ra’ayinmu. Mu ka dinga jifar shi da junanmu da kalmomi kamar “wawa”, “tsohon banza”, “jahili”, “dan iska” da dauransu.
Yanzu kuma, babban Malamin addini (ko ba mu so ba shi ɗin ne) ya yi bayani akan wata matsala, mun watsar da komai da ya faɗa muka kama kalmar “daƙiƙai”. Har waɗansu, abin mamaki harda ɗaliban addini, su na furta kalamai irinna “ɗan iska”, “wawa”,  “jahili”, “ɗan kwangila” akan malamin addinin. Na ga wanda ya yi maganar da ba za ta faɗu ba a nan akan Shehin malamin addini saboda ra’ayin siyasa.
A cikin bayanan da Dr Gumi ya yi, maganar da ta fi jan hankalina ita ce, “ƴan Arewa ba mu da mutum ɗaya (Malamin addini, mai sarauta, ɗan siyasa, ɗan kasuwa da sauransu) da zai ce mu bar faɗa da junanmu, kuma mu saurare shi mu bari”. Ma’ana, babu mutun ɗaya da duk Arewa ke ganin girman shi. Kuma wannan ce-ce-ku-cen da zage-zagen malamai da shugabanni idan sun yi jawabai ya tabbatar da haka.
Wallahil azwim, wannan hali ya na daf da jefa Arewacin ƙasar nan cikin musiba babba da har sai mun yi bauta ga sauran abokan zamanmu nan ba da jimawa ba, idan dai har ba mu gyara ba.
Mu yi hattara!

LEAVE A REPLY