Ado Abdullahi, mai sharhi kan al'amuran yau da kullum
Daga Ado Abdullahi
Ranar Alhamis da ta gabata ne  kwamitin man fetur na majalisar tarayya a karkashin jagorancin shugaban kwamitin Kabiru Marafa ya kira taron masu ruwa da tsaki a harkar samar da man fetur a kasar. A cikin wadanda suka bayyana halin da ake ciki har da karamin ministan mai, wato Mista Ibe Kachikwu inda ya zayyana abubuwa uku da yake ganin su ne maganin matsalar da ake ciki:
1. A baiwa yan kasuwa dama su sayar da mai a duk farashin da suka ga dama, ita kuma NNPC ta sayar a farashin Gwamnati na Naira 145
2. ‎Babban bankin Najeriya wato CBN ya rika baiwa masu shigo da mai Dala daya akan Naira 204 maimakon naira 305 da ake basu domin a cigaba da sayar da man a naira 145 a kowace lita.
3. ‎Gwamnati ta rika biyan tallafi (subsidy) ga duk wanda ya shigo da mai a kowace lita.
Wadannan su ne hanyoyin da shi Karamin minista ya ke ganin zai kawo karshen wahalar mai nan da zuwa watan Yuli na Shekarar badi wato 2019 lokacin da ake sa ran matatar tace mai ta Dangote za ta fara aiki.
To da alamu dai gwamnatin kawo canji da samawa talaka saukin rayuwa ta shiga TSAKA MAI WUYA domin duk shawarwarin da Mista Kachikwu ya kawo babu wacce za ta iya fitar da A’i daga rogo. Idan aka ce a baiwa masu shigo da mai dala akan naira 204 toh ya zama kawai za a kudantar da wasu masu kudi ne, wato an karawa Barno dawaki, inda maimakom su sayo man sun gwammace su sayar da dalar a kasuwar bayan fage wacce farashinta ya kai naira 365,. Domin yin Haldane ya fi shigo da man riba. Idan kuwa aka ce NNPC ce kawai za ta rika sayar da man a farashin Naira 145, su kuma sauran yan kasuwa a farashin da su ka ga dama toh zaune dai ba ta kare ba. Za  a cigaba da ganin dogayen layukan ababen hawa a gidajen mai a duk fadin kasar nan. Idan kuwa aka ce a cigaba da biyan tallafi wato subsidy to an koma gidan jiya kenan wato tsarin da tsohuwar gwamnatin PDP ta yi na kashe makudan kudi don biyan tallafi duk da dai za a rika  samun man cikin rahusa. Ita kuwa gwamnatin canji bai kamata ta ci gaba da kashe makudan kudi don biyan tallafi ba, domin idan aka yi haka an koma gidan jiya kenan.
Toh yanzu menene abin yi?  A cigaba a haka mai yana cigaba da WUYA ko kawai a wuce wurin a yanke farashin man ya koma Naira 180 a kowace lita? Wannan shi ne masana suke ganin shi ne kawai mafita a halin da ake ciki yanzu domin NNPC dai ta ce mai yana zuwa wajen ta ne akan Naira 171 a kowace lita. Dalilin su shi ne a halin yanzu mai ya yi tsada a can inda ake sayoshi, wato kasashen turai. Lokacin da aka yanke za a rika sayar mana da mai akan Naira 145 a kowace lita to farashin danyen mai bai wuce dala 49 a kowace ganga daya ba, yanzu kuwa ya yi daraja ya kai dala 64 a kowace ganga. Wannan shi ya sa yan kasuwa masu sayo man su ka ce matukar ba a kara farashin man ba, su kam ba za su iya ba. Kuma ka da mai karatu ya manta su ne suke shigo da kashi 70 cikin dari na man da ake amfani dashi kasar nan, ita kuma NNPC tana shigo da kashi 30 ne kacal.
Tabbas da alamu babu hanya mafi sauki ta shawo kan matsalar nan illa kawai a mayar da man nan ya koma Naira 180 a kowace lita. Toh amma gwamnati tana jan kafa ne kawai ganin yanzu lokacin yakin neman zabe ya matso, ana neman karin goyon bayan talaka a zango na biyu.  Dole ne a lallaba talakawan da su ka kwana a layi suka gandwala mata kuri’a domin a samu canji. Bayan daman kullum suna zura ido domin jiran ganin sun fara kwankwadar romon democradiyya wanda har yanzu dai romon bai karaso inda su ke ba. Matukar kuma aka kara musu farashin mai toh fa kayan masarufi za su kara yin tashin gwauron zabi fiye da yadda su ke a yanzu. Matukar kuma gwamnatin ta bari aka cigaba da ganin dogon layin mai a duk fadin kasar nan toh lallai kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba kenan, wato canjin dai da ake ta zura ido har mutane su ka fara gajen hakuri bai samu ba kenan.
Toh wai shin yanzu ina mafita?  Ana dara dai ga dare ya yi.

LEAVE A REPLY