Daga Mansur Sokoto
Yau na yi Sallar jum’ah a Masjidus Salam babban Masallacin garin Yamousokrou ta kasar Cote d’Ivoire wanda shugaban kasarsu na farko Felix Houphouet ya gina masu tare da babbar Coci wadda ita ce ta farko ga girma a duniya bayan ta Fafaroma.
Abin mamaki na farko da na gani shi ne yadda aka rako limamin Sheikh Aboubacar Fufana cikin kwambar jama’a suna rera wasu wakoki kamar ana karatun Alkur’ani.
Da shigowar sa ladanin kofar yamma ya fara kiran Sallah shi kuma liman ya dale kan minbari. Yana kammalawa sai ladanin kofar kudu shi ma ya fara nasa kiran Sallar. Da kammalawarsa ladanin kofar arewa ya rera nasa. Hakika da a radio na ji kiran Sallarsu da ba zan gane shi ba domin wata irin waka ce kawai kake ji ana rerawa. Sai an zo karshe sai ka ji Masallacin ya dauka da Sallallahu alaihi wasallam.
Daga nan liman ya hau minbari. Ni ban sani ba da yaren kasarsu ne yake hudubar ko da Faransanci? (Suna da yaren: Abron da Agni da Cabaara Sanufo dss). Amma dai na gane “wattaqullaha” da kuma “kasratuz zunub”… da wasu kalmomi kadan na larabci da ya rika jefawa ko wasu nassoshi da ya kafa hujja da su. A jima kadan kuma sai in ji ana ta ce masa Amin, ni ma sai in ce Amin don kada a bar ni a baya.
Yanzu idan a Najeriya wani limami kuma babba irin wannan ya yi huduba ba da larabci ba za a kwashi rikici wanda sai shekara ta zagayo ba a kare ba kamar dai ita ma huduba irin Alkur’ani ce da ake neman tabarruki da lafazinsa.
Kada ka ce limamin ba ya jin larabci domin yana cikin taron limamai da muke yi kuma na sa shi ya yi larabci mai tsawo kuma mai kyau sosai. Haka ma karatun sallarsa lafiya kalau.
Da ya kare huduba sai ladan ya yi wata hargowa “Safa! Safa!” Sannan aka ta da Sallah aka gama aka yi addu’a.
Masallacin dai kam ya lashi manyan kudi duk da yake an dauki shekaru masu yawa da yin sa amma an zane bangayensa da ginshikansa da wani irin ado mai ban sha’awa irin wanda yake cikin tsohon Masallacin Madina. Abin ban mamaki ace ba Musulmi ne ya gina shi ba.
Asali dai ni na zo halartar taron limamai na Afrika ne da yake gudana yanzu haka a wannan garin wanda ISESSCO ta shirya. Amma na fahimci Allah ne ya hukunta zuwa na domin in karu da albarkar tafiya saboda duk kasashen da aka gayyato masu jin Faransanci ne kawai, kuma sanya ma’aikatar ilimi ta kasar a cikin shirin ya sa aka juya akalar shirin gaba daya zuwa Faransanci.
Amma daga bisani na samu canja yanayin bayan lurar cewa duk limamai ne masu jin larabci kuma aka samu gyara muka koma tattaunawa da harshenmu na Musulunci da ya hada mu.
Fa’ida ta biyu samun haduwa da yan uwa Hausawa da na yi wadanda suka kira ni har unguwarsu na gabatar masu da karatu a daren jiya duk da ruwan sama da ake yi. Yan uwanmu Hausawa na Abidjan tuni sun samu labarin zuwa na tun sauka ta a Airport kuma suna dakon ko zan isa da wuri yau bayan rufe taro domin su ma mu gaisa da su.
Bisa gaskiyar magana, Musulmi yan Najeriya wajibi ne mu gode ma Allah bisa karfin addinin Musulunci da watsuwar karatun Sunnah a cikin mu. Mun wuce wadannan kasashe na faranshi ba kadan ba. Malamai kuma kalubale ne babba a gurguso nan a isar da Da’awa. Allah ya yi muna dace.

LEAVE A REPLY