Auwalu Yusuf Sambo
Daga Auwalu Yusuf Sambo
Mutum 15(Dalibai) aka kashe a Florida(r) kasar amurika amma shugaba (Trump) sai da yayi bayani da nuna alhininsa hadi da jajantawa ga jama’ar da abun ya shafa nan take, bamu san shi gwama da wakilan jama’ar wannan yanki na Florida wane irin alhini, juyayi da gudummuwa suka bawa wadanda wannan matsalar ta faru garesu ba.
A Zamfara(r) Nigeria an kashe mutum kusan 41 amma maimakon muji ko muga gwamnonin kasar kona APC(n) sunje ko sun aika sakon jajantawa ga jama’ar jahar ko gwamnansu, sai ganinsu mukayi a daura harda Abdulazeez Yari(n) sun hallara gaban shugaban kasa(r) Malam Buhari saboda wani abu daya shafi nasu kudurin na siyasa.
Ku gaya mani a wannan matsayar menene banbancinsu dasu Jonathan da Bomb ya tashi a Nnya gari  ya waye suka wuce kano neman jama’a saboda matsalar tasu siyasar?
Kurakurai, rashin gaskiya da rashin adalci da gwamnatin Jonathan takeyi mana sune suka sanya muka tsaneta tare da tsayuwar daka wajan ganin bata kai gaci a zaben daya gabata na kasar ba, wanda a zahirance mukan iya cewa kwautata zato tare da kusancin da muke gani jam’iyyar da jagororin cikinta suna dashi da talakawa wanda hakan ya jingina tunanimmu zuwa ga zato da tsammanin su tawagar APC(n) za sufi kowane bangare na siyasar kasar tausayawa talakawan kasar.
Ka hararo matsaloli da damuwoyi da suka faru a kasar bayan amsar mulkin da wannan gwamnatin tayi, tun daga rikice rikicen da suka faru a karamar hukumar Sardauna dake taraba, ka hararo wanda akeyi yanzu da gobe haka a benue, ka kalli wanda akeyi a kudancin kaduna, mu dubi matsalar data faru a garin Numan, mu hararo wani bangare na cikin garin Adamawa da dai sauran abubuwan da suke faruwa a nan da can din cikin kasar wadanda a kullum mukewa kallon rashin daukan mataki da kokarin dakile matsalar gaba daya da wannan gwamnati taki maida hankali a kai nada gagarumar gudummuwa wajan tabbatuwa daci gaba da lalacewar abubuwa da suke faruwa a kowane bangare na cikin kasar da mukewa kallon ita kadai tallin tal garemu bamu da wata kasar da zamuje muyi yadda mukeso data wuce ta.
Wani abun takaici da damuwa da kullum nake kallo a matsayin koma baya garemu da kasar tamu da muke alfahari da ita, maimakon idan matsala ta tunkaro kasar a taru gaba daya wajan mayar da hankali akan ganin an zaburar da hukuma da wadanda abun ya shafa gaba daya domin kokarin magance ire iren wadannan matsaloli wadanda da kadan kadan dinsu suke farawa zuwa taka matsayin da zasu gagari kowa su addabi kasar da jama’ar cikinta baki daya, sai gaba daya wasu bangare na mutane suka maida al’amarin siyasa ta yadda zaka jisu suna amfani da kalmomin da suke nuna gazawarsu wajan gane abubuwan da ka iya zamewa kasar da ahalinta damuwa da illa ta yadda gaba daya masu hankalin cikin jama’a suke ganin rashin wayewa da karancin sanin lamuran yau da kullum ne suka addabi wani bangare na magoya bayan gwamnati ta yadda basa iya ganin illa bare kuskuren da take dauke dashi wadanda inda aka hada kai domin tunkararsu ka iya zama maslaha a kasar baki daya.
A rashi sanin matsaloli da illolin daka iya zamewa kasar damuwa zaka samesu suna maganganu kan cewa ai duk abunda akeyi bai kai na Boko Haram ba, to tambayar daya kamata muji amsarta daga masu irin wadannan tunanin itace Shin Jira Zamuyi Har Sai Matsalar Takai Ta Boko Haram Kota Wuceta Kafin Mu Nemi Gyara, ko kuwa Mu Sabama Wadan Can Na Farkon Da Suka Saka Ido Matsalar Boko Haram Din Takai Abunda Takai Yanzu bisa daukar matakin daya kamata ya dace shine abunda ya kamata a hada kai ayi.
Lallai akwai rashin wayewa da gogewa kan sanin matsalolin rayuwa ka samu mutum yana maganganu kan cewa ai har yanzu abunda akeyi bai kai na Boko Haram ba, wanda hakan yake zama barazana ga dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankalin jama’ar kasar wanda mukema hakan kallon abunda ka iya jawo nadama da damuwa a kasar nan gaba bada jimawa ba matukar akaci gaba da kallon maganganun wadancan marasa kan gadon a matsayin hujjar barin abubuwa suci gaba da faruwa ba tare da daukar mataki ba.
Tsorona da wannan gwamnatin tazo ta kara dagula lamura wadanda suke faruwa tsakanin dare da yinin kowace rana abubuwa suzo lalace ta kowane bangare, karshe ranar da basu a mulki wanda zai biyo bayansu ya gaji rikici, damuwoyi da fitinar da zata zamewa mulkinsa ala ka kai, daga karshe in zance ya tashi maimakon a jingina laifi da inda ya samo asali sai lissafin mashiririta ya karkace zuwaga wanda mulkin yake hannunsa a lokacin maimakon duba asalin abunda ya jawo matsalar sai laifin ya sauka kan wanda shima a hakan ya tarar da abubuwan, kamar dai yadda Jonathan ya gaji matsalar Boko Haram daga Obasonjo da Yar’adua.
Ina alfahari da kasancewa cikin yan gaba gaba wajan ambata ire iren wadannan abubuwa da suka kasance cikin matsalolin da suka addabi waccan gwamnati data gabata wanda da taimakon Allah mukayi nasarar kaisu kasa da kuru’u da maganganummu, ta bangare daya nakewa Allah godiya daya kaddara mani budaddiyar zuciya da idanuwan da basu rufewa a duk lokacin da bukatar budewarsu ya taso saboda kunyar wani abunda ake iya cewa da gudummuwarsu ya faru, ko kuwa samuwar wata soyayyar rashin dalili ga wata halittar da bata da ikon amfanawa kanta komai bare ta amfanar da waninta Wacce Mai Yinta Bai Amfana Da Ita Ba Ta Kowane Bangare Shima Wanda Akemawa Bai Damu Da Wadanda Suke Masa Ita Ba.
Kuji wata magana ta rashin sanin inda yakema mutum ciwo cikin jikinsa daga wanda al’ummar Zamfara suka zaba matsayin shugaba jagora garesu Wai Ya Fadama Jamio’an Tsaro Wannan Matsalar Zata Faru Kafin Faruwar Matsalar dako kwana nawama yace ohooooo. Dan Allah dan’uwa wannan magana a babin meya kamata mu sakata idan muka kallin wanda ya fadeta, da dalilin daya sanya yafadeta, da abunda ya faru ya fadeta da kuma wadanda yake fadamawa ita, dan Allah yan’uwa mu rika fifita kasa da al’ummarmu sama da abunda muke kallo na kare matsayi da martabarmu.
Hakika gwamnonin Nigeria kun bamu kunya, gaba daya abunda mukayi zato daga gareku babu daya da muke gani, hasalima muna iya cewa zamewarku akan mulki babu abunda ya canza a cikin kasar wanda ya sanya muka zabeku illa kara lalacewar lamura da kara shiriricewar tattalin arziki ta kowane bangare naku. Dukda cewa akwai wasu da muke iya ambata dole daga cikinku wadanda sukayi rawar da za’a iya taruwa a kalla, wadanda jagorancinsu ya amfani jahar da al’ummar cikinta, sai dai in aka ambaceku gaba daya dole bamu da wani abun fada sai hakan domin shine ka’idar dimukuradiya (Majority carry the vote).
Daga Karshe, nake bamu shawara ta bai daya kan cewa koda a siyasance muna ganin fadan wasu maganganun ba zasu yuwu garemu ba, to akwai bukatar mu daina siyasantar da kowane irin zance wanda a gaba zai iya zamewa kasar da al’ummar cikinta damuwa da koma baya ta kowane bangare matukar ba’a taru anyi gyara na bai daya ba.
Allah Ya Bamu Mafita Yayi Mana Jagora

LEAVE A REPLY