Daga Muhammad Sulaiman

Na dade ko ma in ce ban taba ganin abin da ya dugunzuma ni ya bata min rai ya hana ni sakat, ya sa na qara tsorata da lamuran mulki irin na qasata ba, irin wannan videon da ake yadawa na Abba Kyari da irin wannan zaluncin da wallahi ko Fir’uana ne ya yi, tabbas sai an sara masa kuma a jinjina masa. Domin ya yi qoqari. Wato in wannan labarin da su DSP Bulama suka watsa ya tabbata, to a gaskiya gara jakuna da masu irin wancan hali.

Abin da ya faru a taqaice shi ne, a Videon an nuno dan’uwan Abba Kyari wanda da bakinsa da Hausa ya sanar da cewa an ba shi kwangilar kawo motocin Hilux guda 15 a kan kudi miliyan 300. Ya sayar da gidansu na gado da ‘yan sauran kadarorinsa ya karbi bashi a wurin abokai, domin shi ma ya ji almundahanar da za ta sa ya yi kudi.

A qarshe dan”uwansa Abba Kyari, shugaban ma’aikata a fadar gwamnatin tarayya, bayan ya karbe masa ‘yan kudinsa, kuma ya karbe kudin kwangilar, sannan kuma ya sa aka kama su shi da DSP Bulama, wanda bai san hawa ba bai san sauka ba, aka dinga gana musu azaba a ofishin DSS, musamman ma shi Bulama da yake qoqarin gano gaskiya. Sai da ya yi wata biyu a matsayinsa na DSP da riga daya, bayan cin mutuncin da aka yi masa a gaban iyalansa da hankade masa yaro dan shekara biyu. A gaskiya mutumin nan ya ga ibtila’i. Kukansa kawai ya isa ya tayar ma da hankali ya sa ka kuka.

Wato na dade ban kalli Video mai tsawon wannan ba, amma a gaskiya in abin nan ya tabbata, to ba ma ka buqatar ka yi addu’ar Allah Ya yi sakayya. Tabbas Allah zai saka musu. Kuma a gaskiya an ji kunya.

A qarshe abin da na fahimta shi ne, in har abin nan ya zama gaskiya, kamar yadda na fi karkata saboda abin da na ji kuma na gani, to mutanen can fa wato shi dan’uwan Kyarin da DSP Bulama sun fito ne ko a mutu ko a yi rai. Wahalar da suka sha, ta sa a yanzu ba sa shayin mutuwa, domin da ma an riga an gaya musu za a ce su ‘yan BokoHaram ne, kuma an ce wa shi DSP kidnapper.

Ko Baba ne ya kalli wannan Videon sai zuciyarsa ta raunana. Sai dai fa in maqalutu aka rataya mata.

Ya Allah Ka shiga tsakanin nagari da mugu, Ka kawo mana dauki a wannan miskiniyar qasar tamu, amin.

LEAVE A REPLY