Marubuci,Bello Habeeb Galadanchi
Bello Galadanchi
Sakamakon neman ilimi da nake yi a manyan kasashe biyu na duniya, da kuma zagaye sama da kasashe goma sha bakwai a duniya, na hadu da jama’a masu yawan gaske, kuma na koyi abubuwa da dama daga wajensu. Na bude kamfani na farko a Amurka ina da shekaru 21, sannan na samu aiki a Muryar Amurka ina da shekaru 24. Na kuma bude makaranta tawa ta kaina ina da shekaru 28. Na yi nasara a wasu harkokin, wasu kuma na fadi, lamuran da suka koya mun darusa da yawa na rayuwa. Sakamakon wadannan hawa da sauka, da kuma haduwa da mutane da yawa wadanda suka yi nasara, a nawa ra’ayin akwai  manya-manyan dabi’u guda hudu.
1.BASU KWAIKWAYAR SAURAN JAMA’A, SAI DAI A KWAIWAKYE SU: Abubuwan da sauran jama’a suke yi basu harzuka su. Kullum tunaninsu shine ta yaya za’a inganta wadannan abubuwa? Sun fi mayar da hankali akan abubuwan dake da nakasu, kuma al-umma bata ankara ba, da kuma irin alherin da za’a samu daga warware wadannan matsaloli. Da sun gama fahimtar haka, sai su hau aiki.
2.SUN SAN ABUBUWAN DA SUKA IYA: Masu nasara a rayuwa sunfi mayar da hankalinsu akan abubuwan da suka riga suka iya, da kuma watsi da inda suke da matsala. Abunda suke yi shine kara himma da kwazo wajen kwarancewa da lakantar abubuwan da suka iya, domin su fi kowa.
3.SUN IYA HADA HAZAKA DA BAIWA: Kowa a duniyannan yana da irin nashi baiwa. Su mutanen dake nasara a rayuwa na fahimtar baiwar su, sannan su kasance masu aiki tukuru domin inganta ta, da kuma gani ta warware matsalolin alumma.
4.DOGARO DA ALLAH: Mutanen dake nasara sun fahimci cewa duk kwazonsu, dole sai sun hada da ibada. Sun san cewa addu’a bata aiki idan mutum bai mike tsaye ya nemi abunda yake bukata ba. Saboda haka sun fi kowa addu’a, kuma sun fi kowa kwazo.
Ga misali. Hajiya Aisha ta iya dafa abinci (2. SUN SAN ABUBUWA DA SUKA IYA), saboda haka, ta yanke shawarar bude sabon gidan abinci na zamani. Amma abunda ta lura da shi shine, gidajen abinci suna da matukar yawa, saboda haka ta yaya zata banbance nata da na sauran mutanen garin baki daya? (BASU KWAIKWAYAR SAURAN JAMA’A, SAI DAI A KWAIWAKYE SU) Hajiya Aisha ta lura cewa jama’a da yawa suna zuwa gidan abinci, amma sai ruwan ido ya hana su zaben abunda suke so. An riga an yanke musu shawara, sai dai su zabi irin abincin da suke so, masu dafawa su dafa. Ita kuma, sai ta kirkiri wani sabon tsari. Tsarin shine duka kayan abincin da ba’a dafa ba suna waje, an jera su a cikin gilashi. Naman kaza ne, salak ne, neman rago, ganda, karas ne, doya, dankali, shinkafa, taliya, wake da sauransu. Wato idan kwastoma ya shigo, sai ya dauki fanteka, ya zabi duk abunda yake so da hannunsa, iya adadin da yake so, sannan a auna akan sikeli, ya biya. Hakan kuwa ya baiwa jama’a sabon salo na sayen abinci, kuma an warware matsalar masu ruwan ido. Mutum zai iya cin duk wani irin abinci dake wannan shago, iya adadin da yake so, ba tare da kashe kudi ya sayi ire-iren abinci biyu ko uku ba. Zai iya hada naman rago, naman kaza, taliya da karas. Wani kuma idan ya tashi, sai ya hada kifi, salak, shinkafa da taliya. Ba’ayi watanni uku ba, duk labari ya baza gari na wannan sabon gidan abinci mai baiwa jama’a ‘yanci, lamarin da yayi sanadiyar cincirindon kwastomomi har daga bayan gari. Don ta bunkasa sana’arta (SUN IYA HADA BAIWA DA HAZAKA), kullum karfe biyar take tashi da asuba ta fara shirya kayan abinci, ta tabbatar an wanke shagon kuma ta aikawa kwastomominta gaisuwa a shafinta na WhatsApp, da kuma irin sabon kayan abinci da zata kawo a wannan rana.
Wannan labarin kirkirarshi nayi. Idan akwai wanda yake sha’awar wannan sana’a, to sai ya tuntube ni domin zurfafa tunani da fasalta shi yadda za’a samu alheri.

LEAVE A REPLY