Hadiza Gabon

Daga Abba Ibrahim Wada

Shahararriyar yar film din Hausa Hadiza Gabon ta mayarwa da wani mai binta a shafin Twitter martani bayan da tasaka wani hoto, shi kuma ya tanka.

Hadiza gabon, wacce ’yar asalin kasar Gabon ce, a kwana kwanannan tafara fitowa a fina finan turanci na industirin Nollywood.

A ranar ashirin ga watan nan ne dai jarumar ta saka wani hotonta a shafinta na Twitter kamar yadda saba.

Tsokacin da wannan bawan Allah mai suna M. Bash ya yi a kan hoton inda ya ce: “Masha Allah an girma ai yakamata a fidda mijin aure”, ya ja masa martani a cikin kakkausar murya daga jarumar.

Cikin fushi Hadiza ta zabura ita ma ta mayar da nata martanin cewa: “To ko zaka bawa tsoho shawaran ya ma tsohuwa retire ya kawo ni ne?”

Jaruma Hadiza Gabon dai ta dade tana fitowa a fina-finan hausa, wasu daga cikin fina-finanta da sukafi shahara sun hada da ’Yar maye da Gwaska na jarimi Adam A. Zango.

Shin martanin da ta ba shi ya dace?

LEAVE A REPLY