Tsohon Gwamnana jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewar zai zo Kano a ranar 30 ga watan Janairu, duk abinda zai faru sai dai ya faru, yace kuma duk wani abu da ya faru, to kwamishinana ‘yan sandan jihar Rabiu Yusuf shi ne ke da alhaki ba wani ba.

A ranar juma’a Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, ya shawarci Mista Kwankwaso da ya watsar da batun zuwansa Kano a ranar 30 ga watan nan da muke ciki, biyo bayan rahotannin tsaro da rundunar ‘yan sandan jihar ta samu.

Sanata Kwankwaso, wanda yayi magana ta hannu tsohon Sakataren Gwamnatinsa, Rabiu Suleiman Bichi a ranar Asabar, yace, Kwamishinan ‘yan sanda ya zama dan amshin shatar Gwamna Ganduje ne kawai.

Yace, Kwamishinonin Gwamnatin Ganduje, tare da wani mutum da yake kiran kansa jagoran yakin neman zaben Shugaba Buhari,mai suna Abdulmajid Danbilki Kwamanda sune suke cewar sai sunyi duk abinda zasu yi don su hana Kwankwaso zuwa Kano.

“A ranar 16 ga watan Disamba, 2017, da kuma 15 ga watan Janairun nan, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya bayyana balo balo a Radiyo cewar, ba zasu taba barin Kwankwaso ya shigo Kano ba, inda yace duk ranar da ya bayar zai shigo suma sai sun shirya taro a ranar dan ta ci karo da zuwan Kwankwason”

“Haka nan, shima, Abdulmajid Danbilki Kwamanda an jiyoshi a Radiyo Aminci, yana bayyana cewar zasu sanya a kama Kwankwaso matukar ya shigo Kano”

 

LEAVE A REPLY