Daga Hassan Y.A. Malik

Akalla mutane 6 ne ciki har da malaman makaranta 2 da ke aiki da hukumar ilimi ta karamar hukumar Makurdi ne fulani makiyaya suka kashe a kusa da Ikpayongo da ke karamar hukumar Gwer a jihar Binuwai.

Rahotanni sun bayyana cewa wadanda aka kashe din na daga cikin mutane goman da suka tafi gonarsu ta shinkafa a karkashin wata kungiyar taimakon kai-da-kai tasu.

Hudu daga cikin malaman sun kai da kafafuwansu da kyar, inda ragowar mutum shudan kuma suka fada hannun fulani makiyayan, inda suka kashesu bayan nan kuma suka yi gundu-gunduwa da su.

An gano gawar wadanda aka kashe din ne a ranar Alhamis din da ta gabata da taimakon jami’an tsaro.

Wata majiya daga yankin da abin ya faru ta bayyana sunayen malaman biyu da suka rasa rayukansu da: Mista Stephen Tavaku, wanda hedimasta ne a makarantar Firamare ta St. Mary da ke Makurdi, da kuma Mista Christian Anankpa, wanda dalibin digiri na uku ne a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zari’a kuma malamin ilimin kimiyya ta karamar sakandiren St. Mary da ke Makurdi.

Wani abokin aikin Mista Tavaku mai suna Emerald Anyaogu ya bayyanawa manea labarai cewa, “Ban taba zata haduwa da Tavaku a ofishinsa ita ce haduwarmu ta karshe ba a ranar da abin ya faru.”

Shi ma wani abokin aikin maragayi Anankpa ya ce, “Mutane 10 wadanda 4 daga ciki malaman makaranta ne suka kafa wannan kungiya ta taimakon kai-da-kai ta hanyar noma, kuma sun tafi duba gonar shinkafar tasu ne a lokacin da fulani makiyayan suka yi musu dirar mikiya.”

LEAVE A REPLY