Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru el-Rufai

Daga Hassan Y.A. Malik

Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sheghu Sani ya yi alwashin tsayawa neman kujerar gwamna jihar Kaduna a zaben 2019 don karawa da gwamna Malam Nasir El-rufa’i.

Sanata Sani ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da jaridar Guradian a karshen makon da ya gabata, inda a hirar ya yi Allah wadai da zaben kananan hukumomin jihar Kaduna.

“Sam sakamakon zabukan kananan hukumomin jihar Kaduna bai yi daidai da ainahin abinda ya faru a lokacin zaben ba.

“Haka kuma ba a gudanar da zaben shugabannin jam’iyya ba a jihar Kaduna, sunaye kawai aka rubuta aka tura shedikwatar jam’iyya ta kasa, kuma yin hakan ya janyo rikicin cikin gida musamman ma wadanda suka sayi fom don neman kujeru.

“Ina so Gwamna El-rufa’i ya sani cewa zan buga da shi a fagen neman gwamnan jihar a shekarar zabe mai zuwa ta 2019 kuma ya sani cewa ba hukumar zabe ta jiha ba ce za ta gudanar da wannan zabe,” inji Shehu Sani.

Sanata Sani ya ci gaba da cewa ko shakka babu kashe-kashen da Boko Haram da fulani makiyaya ke ci gaba da aiwatarwa akan talakawan Nijeriya zai yi tasiri a zaben shugaban kasa da na gwamnonin wasu jihohin Nijeriya.

LEAVE A REPLY