Sule Lamido
Tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido , da yammacin ranar jiya a Abuja ya kai ziyarar ta’aziyyar rasuwar tsohon shugaban babban bankin Nigeria, tsohon minista sau uku kuma d’aya daga cikin mutane 9 da suka kafa jam’Iyyar PDP a Najeriya Dattijo Malam Adamu Chiroma wadda Allah ya yiwa rasuwa bayan fama da doguwar rashin lafiya
A d’aya bangaren jagoran ya mik’a sak’on ta’aziyya ga al’ummar Babura, Masauratar Ringim da al’ummar jihar Jigawa bisa ga rasuwar Hakimin Babura Sarkin Ban Ringim, Alhaji Hadi Mustapha Babura, wadda Allah ya yiwa rasuwa da safiyar jiya.
Lamido ya bayyana wannan rashi da cewar babban rashi ne ga al’ummar musulmi Idan aka yi la’akari da irin gudunmawar da suka bayar a tsawon rayuwarsu, za’a jima ana amfana da alheran da suka shuka kuma al’umma take amfana dashi a koyaushe
Jagoran ya bayyana jimaminsa yayin da ya samu sak’on wannan babban rashi na yan k’asa na gari ya bayyana rasuwar su da cewar ba rashi ne na iyalai da yan uwa ba, rashi ne na al’ummar Nigeria.
Yayi fata tare da addu’ar Allah ya jik’ansu da rahama, ya gafarta musu zunubansu, ya haskaka k’abarinsu ya sa aljanna ta zama makoma a gare su da sauran al’ummar musulmi baki d’aya
Mansur Ahmed
New media aide to
Dr. Sule Lamido CON

LEAVE A REPLY