Mataimakin Gwamnan jihar Zamfara Malam Ibrahim Wakkala ya bayyana aniyarsa ta yin takarar Gwamnan jihar a zaben 2019.

Idan ba a manta ba Gwamnan jihar Abdulaziz Yari ya bayyana goyon bayansa ya kwamishinan kudin jihar Mukhtar Idris a matsayin wanda zai marawa baya.

Dama dai tuni jam’iyyar APC a jihar ta bayyana cewar dantakarar Gwamnan jihar a wannan zaben zai fito daga yankin Zamfara ta tsakiya inda Wakkala da Mukhtar suka fito.

Wannan dai alamu ne dake nuna cewar za a yi zazzafar Siyasa a jihar Zamfara tsakanin Bangaren tsohon Gwamna Yarima Bakura da kuma bangaren Gwamna Abdulaziz Yari.

LEAVE A REPLY