Zakaran damben duniya, Floyd Mayweather

Daga Hassan Y.A. Malik

Daya daga cikin masu tsaron lafiyar zakaran damben duniya, Floyd Mayweather ya samu raunika a yayin da wani dan bindiga a cikin mota ya budewa motar dan danben wuta a ranar Litinin din da ta gabata a jihar Atlanta ta kasar Amurka, kamar yadda ‘yan sanda suka rawaito.

Sai dai, a yayin da maharin ya kai hari kan motar Mayweather, dan damben ba ya cikin motar, a saboda haka bai samu wani rauni ba a ta bakin kakakin rundunar ‘yan sanda jihar Atlanta.

Mai tsaron lafiyar Mayweather, Gregory LaRosa, ya samu rauni a kafarsa bayan harsashi ya same shi daga harbin maharin, kuma har an sallamo shi daga asibiti awanni 3 kacal bayan harbin nasa.

Mayweather da mukarrabansa a yammacin ranar da abin ya faru sun halarci wani gidan rawa, inda daga bisani ayarin motocin dan danben (motoci kirar jif guda 3) ya halarci wani wajen cin abinci, inda a nan ne maharin ya budewa jerin gwanon motocin na Mayweather wuta.

‘Yan sanda Atlanta sun bayyana cewa lalle maharin Mayweather ya nufa da harinsa domin da alama ya san motocin da kuma mai su, sai dai ‘yan sandan sun bayyana cewa basu da masaniya na cewa ko wani abu ya faru tsakanin Mayweather da wasu mutane a yammacin ranar ta Litini da abun ya faru.

Mayweather, wanda ya bayyana yin ritaya daga dambe a watan Ogustan bara bayan ya doke Conor McGregor ya halarci Atlanta ne don gabatar da wani kanfen na harkokin dambe a Las Vegas.

LEAVE A REPLY