A kalla mutane shida ne suka rigamu gidan gaskiya sakamakon wata zaftarewar kasa da ta auku a kauyen Illela-Kalmalo a yankin karamar hukumar mulkin Illela dake jihar Sakkwato, Kamfann dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito hakan.

Lamarin dai ya auku ne a lokacin da mutanen suke tonon kasa, domin taya wani abokinsu ginin gidan da zai zauna a yunkurinsa na yin aure.

Wani da abin ya faru akan idonsa, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, cewar wani mutum guda ya samu damar kubuta lokacin da kasa ta zaftaro ta rufe su.

An bayyana sunayen mutanen da suka rasu da Bashar Dalhatu da Bashar Maciji da Bashar Buhari da Isah Amadu da Abdullahi Salihu da kuma Bilyaminu Jadi.

Shaidar ya kara da cewar, tuni aka binne mutanen a kauyen kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

“Yana daga cikin al’adarmu a wannan kauyen, duk lokacin da wani zai yi auren fari, abokansa zasu hadu domin su taya shi tono kasa da kuma gina gidan da zai zauna, bayan sauran taimako da suke bashi”

“Muna yin hakan ne domin saukakawa mutum radadin kashe kudin da zai yi na bikin aurensa”

“Biisa tsautsayi, a lokacin da suke tono kasa domin wannan aikin gayya da zasu taya abokinsu, sai kawai kasa ta rufta da su, daga bisani muka tono gawarwakinsu, muka kuma yi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar” Daya daga cikin mazaunan kauyen ne ya bayyana hakan.

Shugaban karamar hukumar Illela, Alhaji Abdullahi Haruna-Illela ya tabbatar da aukuwar wannan lamarin a yankin karamar hukumarsa.

LEAVE A REPLY