Hon. Muhammad Gudaji Kazaure

Dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazabar Kazaure da Roni da Gwiwa da Yankwashi a majalisar wakilai ta kasa, Hon. Gudaji Kazaure ya bayyana cewar matukar aka yi yunkurin tsige Shugaban kasa Muhammadu Buhari daga kan karagar mulkin kasarnan to ba shakka an ballo gagarumin yaki.

Idan za’a iya tunawa, a ranar Talatar nan ne, ‘yan majalisun tarayya da na sanatoci suka yi wani zaman na hadin guiwa tsakaninsu, inda suka fitar da wasu kudurori guda goma sha biyu, inda suka yi kira ga Shugaban kasa ya yi wani abu akai, ko ya fuskanci fushinsu.

Sai dai kuma a lokacin da yake tattaunawa da ‘yan jaridu bayan kammala wancan taron, Gudaji Kazaure, ya bayyana cewar zasu yaki duk wani yunkuri na yiwa Shugaban Buhari karan tsaye ko kuma tunanin tsige shi, wanda a cewarsa daura yaki ne kiran cewar a tsige Buhari.

“Babu wanda ya isa ya tsige Shugaba Buhari a matsayinsa na Shugaban kasa matukar muna nan da ranmu a wannan majalisar. Wannan lokacin kuwa lokaci ne na yaki tunanin tsige Shugaba Buhari” A cewar Gudaji Kazaure.

 

LEAVE A REPLY