Daga Ado AbdullahiA lokacin da al’umma ta shashance ta zama TALAUCI da JAHILCI sun yi mata katutu.

Lokacin da suke wulaƙanta kansu wajen kyale mutumin kirki, nagartacce, ƙwararre da amana a gefe. Suka gwammace a ba su kuɗi su zaɓi mutanen banza.

Lokacin da suke rigengeniyar karɓar kuɗi don zaɓen waɗanda za su damƙawa amanar rayuwarsu. Waɗanda sun sani sarai ana tuhumarsu da al’mundahana da satar kuɗin al’umma ko kuma sun yaudaresu a baya sun sace kuɗaɗen Jihohinsu.

Duk lokacin da al’umma ta zama haka toh dole wannan al’umma ta shiga ruɗani, firgici da rashin tabbas a duk al’amuranta.

Wai yaushe ne al’ummarmu za ta waye ta fita daga ƙangin bautar masu mulki, mayaudaran ƴan siyasa, maha’inta, ƴan babakere. Masu siyasar sayen ƴancin talaka da tursasashi da barazana da firgita al’umma da ƴan sara-suka, alhali ƴaƴansu suna kulle a gida ko sun tura su karatu ƙasashen ƙetare?

Sai wane lokaci ne talaka zai farka ya san cewar waɗannan ƴan siyasar da ake ɓata dare da rana wajen kare muradunsu, ba su damu da rayuwar al’umma ba, basu damu da makomar matasansu ba. Basu damu da ilmin waɗanda suka zaɓe su ba.

Duk lokacin da rashin lafiya ta kama wasunsu, kai wasu ko sayen kayan lefen bikin ƴaƴansu za a yi, sai sun dangana da ƙasar waje. Amma sun bar al’umma babu ilmi ingantacce, babu ruwan sha mai tsafta, babu asibiti nagartacce babu wani aikin yi na azo a gani. Babu……babu….. babun ba za ta lissafu ba.

Shi kuwa bawan Allah talakan sai ana daf da shiga zaɓe, sai a riƙa ribatarsa da ɗan kayan masarufin da ba zai kai shi kwana biyu ba. Ana raba musu ledar taliya guda ɗaya. Ko a basu kwalin sabulu ko biredi leda ɗaya, wasu ma da kwalin ashana ake sayensu. Ƙiri-ƙiri mun gani ana sayen ƙuri’ar talaka a kan naira 200 kacal.

Baya ga wannan yaudarar da zaluncin kuma fa, ƴaƴan wannan talakan ne ƴan siyasa suke amfani dasu wajen maguɗin zaɓe domin su ci gaba da mulkin kama karya da danne haƙƙin iyayensa, yayyensa da ƙannensa. Da shi dai ake amfani su riƙa kashe junansu alhalin mai yiwuwa wanda ya haddasa rikicin ma yana kwance a kan gadonsa zagaye da jami’an tsaro cikin kwanciyar hankali.

Wajibi ne al’umma ta farka daga ɗimuwa da rashin wayewa da rashin kwaɗayi domin neman ƴancin kanta daga azzaluman ƴan siyasa waɗanda kansu kaɗai suka sani.

Wajibi ne a dawo a sake tunani a zaɓo mutanen kirki a duk matakin da suka tsaya zaɓe. Ba tare da la’akari da sun fito a ƙaramar jam’iyya ba, ko kuma basu da kuɗin da zasu raba don a zaɓesu.

Lokaci ya yi da talakan ƙasar nan zai fara zaƙulo mutanen kirki masu son cigaban yankunansu domin su tsayar dasu takara a kowace jam’iyya ce domin samun shugabanci nagari da bijirewa tsarin kama-karya na mugaye ƴan siyasa marasa kishin ƙasa.

Ado Abdullahi
19-03-2019


LEAVE A REPLY