Daga Hassan Y.A. Malik

Wani yaro dan shekaru 8 da haihuwa da aka bayyana sunansa da Sadi Yusuf ya rasa ransa a safiyar yau Talata sakamakon fadawa rijiya da ya yi a garin Tamburawa Gabas a jihar Kano.

Kakakin jami’an ‘yan kwana-kwana a jihar Kano, Alhaji Sa’idu Muhammad ne ya bayyana kamfanin dillancin labarai ta kasa, NAN, afkuwar lamarin da misalin karfe 7:30 na safiyar yau.

Mahaifiyar yaron ce ta aike shi diban ruwa a rijaya da sanyin safiyar yau din, inda a nan ne tsautsayi ya sa ya fada rijiyar.

“Mun samu waya daga mai unguwar Tamburawa Gabas din, Malam Isa Garba, da misalin karfe 7:30 na safe, inda ya shaida mana cewa yaro ya fada rijiya.

“Ko da samun wannan rahoto sai muka gaggauta aikewa da jami’anmu na agaji zuwa garin, kuma sun isa da misalin karfe 7:42.

“Jami’anmu sun ceto yaron ba a cikin hayyacinsa, inda suka mika shi a hannun mai unguwa Isa Garba, kafn daga baya ya ce ga garinku nan,” Kakakin na ‘yan kwana-kwana ya fada.

Kakakin ya yi kira ga iyaye da su daure su daga bakin rijiyoyinsu kana kuma su yi usu murfi don kare afkuwar hadurra irin wannan a gaba.

LEAVE A REPLY