RUndunar ‘yan sandan jihar Legas ta cafke wata matashiya ‘yar shekaru 19 mai suna Dorcas Adilewa, wadda ta shirya cewar anyi garkuwa da ita domin ta damfari mahaifinta.

Kamfanin dillancin labari na Najeriya, NAN, shi ne ya ruwaito hakan, ina ya bayyana cewar yarinyar wadda ta hada baki da wani abokinta mai suna Ifeoluwa Ogunbanjo wanda shi ne ya shirya inda suka boye yarinyar kuma yayi magana da iyayenta ta wayar tarho.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, Imohimi Edgal, ya tabbatar da cewar an kama yaran ne a ranar 13 gawan Yuli bayan wasu bayanai sirri da suka samu daga mahaifin yarinyar a caji ofis din ‘yan sanda dake Ketu a jihar Legas.

“A ranar 7 ga watan Yuli da misalin karfe 5 na yamma, Adilewa Taiwo dake gida mai lamba 3 a Layin Kosumi a ynguwar Bello-Keto a jihar Legas ya shaidawa caji ofis na ‘yan sanda dake Ketu, inda yace an kirashi da wata lamba 09057432362”

“Mutumin yace an shaida masa cewar an yi garkuwa da ‘yarsa mai suna Dorcas Adilewa, kuma idan baya son a kashe ta, tilas ya biya kudin fansa Naira 600,000 domin a sake ta”

“Ba tare da wani bata lokaci ba ‘yan sanda suka shiga bincike kan lamarin,inda bincikensu ya gano musu cewar lambar wayar  da aka yi amfani da ita, mai maganar yana unguwar Ijebu-Igbo a yankin jihar Ogun”

“Dan sanda mai lura da sashin kula da masu garkuwa da mutane, ya jagoranci wata tawaga da suka tasarwa yankin da lambar wayar take domin kamo wadan da ake zargi, inda suka ci nasara damke su”

 

LEAVE A REPLY