Wasu yara biyu sun nitse a wani kududdufi a kauyen Gantsa dake yankin karamar hukumar Buji a jihar Jigawa.

Adamu Shehu, kakakin rundunar tsaro ta NSCDC, shi ne ya tabbatar da faruwar wannan al’amarri ga kamfanin dillanccin labarai na Najeriya, NAN, a ranar Juma’a a birnin Dutse.

Shehu ya shaidawa kamfanin dillancin labaran cewar lamarin ya auku ne a ranar Alhamis da misalin karfe 6 na yamma yayin da yaran ke wasan linkaya.

An bayyana sunayen yara Yusuf Adamu dan shekara 6 da kuma Umar Ibrahim mai shekara 4, yace likitoci ne suka tabbatar da rasuwar yaran guda biyu, yayin da aka garzaya da su asibti domin basu agajin gaggawa.

 

LEAVE A REPLY