Wata ‘yar shekara 13 da haihuwa da ake zargin wasu maza 8, cikinsu har da limami da yi wa fyade a karamar hukumar Kubau ta jihar Kaduna na dauke da cikin wata 5 na ‘yan tagwaye.

Shugabar gidauniyar Arridah, Malama Rabi Salisu ce ta shaidawa kamfanin dillacin labarai na NAN wannan batu bayan da aka kawo yarinyar ga kungiyar don su taimaka wajen an tabbatar da adalci wajen hukunta wadannan mutane da suka aikata ta’annati akan yarinyar.

Malama Rabi ta bayyanawa kamfanin dillacin labarai cewa, kungiyarta za ta nemi goyon baya daga duk inda ya dace, sannan kuma ta bi shari’ar a kotu har sai ta tabbatar da cewa yarinyar ta samu adalci.

A binciken da kamfanin dillacin labaran ya gudanar, an gano cewa shi dai wannan limami wanda yake daya daga cikin wadanda ake zargi da yi wa yarinyar fyade makwabcin su yarinyar ne.

Malama Rabi ta ci gaba da cewa a tsawon lokacin da muka shafe muna fafutukar yaki da tauye hakki da cin zarafi, mun karbi koke har guda 400 kuma da yawa daga cikinsu koke ne akan fyade da cin zarafin kananan yara, amma ba mu taba cin karo da tsantsar rashin imani irin wanda wadannan mutane suka shuka akan wannan yarinya ba.

“Abin tausayi ne yau a ce maza 8 jibga-jibga na aikata fyade akan yarinya ‘yar shekara 13 da ko kirgan dangi bata fara ba. Yanzu ga shi tana da cikin ‘yan tagwaye a daya hannun kuma iyayenta na ikirarin sai sun zubar da cikin don gudun abin kunya.

“Mazaje takwas fa! Yarinyar na iya daukar cutar karya garkuwar jiki (HIV/AIDS) da sauran cututtukan da ake dauka ta hanyar jima’i musamman idan an yi saduwar ba tare da son rai ba.
“Muna nemawa wannan yarinya adalci kuma a kokarinmu na ganin ta samu adalci, muna neman hadin kan gwamnatin jihar Kaduna, kungiyoyin kare hakkin bil adama, kungiyoyin addinai da shugabannin addinai da su shiga cikin wannan magana don ganin yarinyar nan ta samu adalci,” a cewar Malama Rabi.
Mahaifin yarinyar, Malam Mu’azu Shittu ya bayyana cewa tuni dai ya yi karar wadannan mutane da suka ci zarafin ‘yarsa a kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a Ikara.
A cewarsa, ya yi yunkurin ya zubar da cikin amma sai aka shawarce shi da kar ya kuskura ya aikata hakan.
“Ta yi kankanta ta dauki cikin tagwaye kuma abin takaicin shi ne babu daya daga cikin mutane 8 din da suka yi mata fyaden da ya yadda ya kula da dawainiyarta da na abinda ke cikinta,” Malam Mu’azu ya koka.
A ta bakin yarinyar, ta ce suna bata naira dari biyar sannan kuma su ja kunnenta da cewa kar ta yarda ta fadawa kowa.
“Su suke kirana su bani N500 in na dawo daga makaranta in an dora min talla. Dole suke yi min.
“Kuma sun min gargadi da kar na fadawa kowa kuma in har na fadawa iyayena, to, za su kasheni, shi yasa ma ban taba fadawa kowa ba saboda ina tsoro,” a cewar yarinyar.

LEAVE A REPLY