Kimanin mako guda bayan da sugaban rundunar sojojin kasa ta Najeriya, Lutanar Tukar Burtai ya baiwa sojoji umarnin zama a garin Birnin-Gwari har sai zaman lafiya ya dawo yankin, a lokacin da ya ziyarci yankin sakamakon yawan tashe tashen hankula da ake samu a garin na Birnin Gwari da kauyukan dake yankin.

Sai dai kuma, da sanyin safiyar ranar Asabar, aka samu ‘yan ta’adda suka shiga kauyen Maganda dake yankin na Birnin Gwari, inda suka sace wasu matan aure guda uku suka yi garkuwa da su.

Wani dan kungiyar sa kai ta sintiri a yankin na birnin Gwari wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaidawa majiyar PRNigeria cewar maharan sun shigo cikin garin maganda ne da tsakar dare inda suka sace matan suka yi garkuwa da su.

“Maharan sun shigo kauyen an Maganda da misalin karfe 1:30 na dare inda suka dinga harbin kan mai uwa da wabi a sararin sama, inda daga bisani kuma suka yiwa gidan wani Alhaji Adamu Nakwalla tsinke, anan ne suka sace matansa guda uku suka yi garkuwa da su.”

“Lallai kafin wadannan ‘yan ta’adda su shigo garin na Maganda a Birnin-Gwari sai da suka aiko da sakon gargadi ga mutanan kauyen cewar zasu shigo kauyen ba da jimawa ba”

“Babu labarin wani wanda ya rasa ransa a yankin, sai dai an samu wani matashi da ya samu rauni a sakamakon harbin bingida”

 

LEAVE A REPLY