Orji Kalu

Daga Hassan AbdulMalik

Tsohon gwamnan jahar Abia, Orji Uzor Kalu ya tabbatar da cewa ‘yan siyasar Nijeriya ne ke daukar nauyin kungiyar Boko Haram da sauran rikice rikicen da ake samu a kasar nan.

Kalu ya fadi haka ne a gidan shi da ke jahar Abia, bayan wata ganawa da ya yi da mambobin jam’iyyar APC reshen jahar, inda suka tattauna yadda za su karfafa jam’iyyar a jahar.

Ya ce ya yi imanin cewa shugaba Buhari zai samu nasara akan mayakan Boko Haram duba da kasancewar shi tsohon soja.

A cewar shi “Shugaba Buhari janaral ne na soja; ya fuskanci menene yaki. Ya na kallon lamarin ne a matsayin shi na kwamanda, kamar yadda kuke gani, fada da Boko Haram kamar yaki ya ke”

Ya dora alhakin abubuwan tashin hankali da ke faruwa a kasar nan a kan bata garin ‘yan siyasa, inda ya yi kira a gare su da daina tun kafin doka ta hau kan su.

 

LEAVE A REPLY