Shugaba Muhammadu Buhari

‘Yan siyasa da masu sharhi kan al’amuran yau da kullum sun yi hannun riga da kalaman Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan batun da ya tayar lokacin da yayi jawabi ga al’ummar Najeriya a ranar daya ga watan sabuwar shekarar nan. Inda Shugaban yace, matsalar Najeriya bata ta’allaka kan batun sake fasali ba, illa kawai rashin hakuri na mutane a cewarsa.

Shugaban Buhari, a lokacin da ya gabatar da jawabin ga al’ummar kasa, yace ra’ayinsa kan batun da ake ta yayatawa na a sake fasalta Najeriya, yace dukka matsalolin kasarnan ba su wuce rashin hakuri na mutane ba.

Sai dai kuma, ‘yan Siyasa da kuma masu sharhi kan al’amuran yau da kullum sun caccaki kalaman Shugaba Buharin a wata zantawa da suka yi da kamfanin dillancin labarai na Najeriya a birnin Legas a ranar Alhamis.

Martin Onovo, wanda ya taba tsayawa takarar Shugaban kasa a karkashin jam’iyyar NCP, ya bayyana cewar, rashin adalci ne ace wai ‘yan Najeriya sun cika gajen hakuri.

“Dukkan matsalolin da suke damun kasarnan galibinsu sun shafi Shugabanci ne, da kuma batun cin hanci da rashawa da yayiwa kasar daurin butar Malam. A sabida ba haka, ba daidai ne a zargi cewar mutanen Najeriya sune ba suda hakurin ba”

Mista Onovo ya kuma bukaci Shugaba Buhari da ya cika alkawuran da yayiwa ‘yan Najeriya lokacin yakin neman zabe.

MadamJoe Okei-Odumakin, Shugaban kungiyar rajin kare mata da kawo sauyi, ta bayyana cewar, rashin tafiya kan tsarin da Shugabanni suke yi shi ne silar lalacewar al’amura a kasarnan.

“Yana da wahalar gaske, ka iya gamsar da mutane yadda kake so matukar ana kaucewa bin tsari da ka’ida, tilas ne abi duk abinda aka shimfida sau da kafa in ana son ganin daidai”

“Ana cakuda takardu sosai a al’amuran kasarnan. Dole ne Najeriya tabi dukkan tsarin da magabata suka dorata a kai, domin samun abinda zai fisshemu, sannan watakila daga baya a iya zuwa da batun da ake so na kawo gyara ko sauyi”

Musa Umar, wani jigo a cikin jam’iyyar APC reshen jihar Kano, ya bukaci ‘yan Najeriya da su yiwa batun sake fasalta kasarnan kyakkyawar lura.

“Batun sake fasalta kasarnan da ake yamadidi da shi, sam ‘yan Najeriya basu fahimci abin ba ma. Batu ake fa na, rabon mukamai da rabon tattalin arzikin kasa da kuma su waye suke da iko da arzikin da ke yankunan su da kuma batun daga wacce shiya Shugaban Najeriya ya kamata ya fito”

“Dukkan halin da ake ciki a wannan kasa koma meye dai, muna bukatar sake samun fasali, dole ayi hakan domin zai fi zama adalci kan batun sake fasalta Najeriya”

“Haka kuma, kasancewar Najeriya na bin turbar demokaradiyya, idan har mafi rinjayen ‘yan Najeriya sun bukaci sake fasalta kasarnan, to abinda ya fi kamata ayi kenan, barin guntun kashi a ciki ba zai taba maganin yunwa ba”

“Fargaba ta shi ne, idan har muka gaza samun canjin da ake bukata, to ba zamu taba gamsar da mutane kan abinda suke so ba, domin kuwa za a yi uwar watsi nan gaba da alama, to dan haka wa gari ya waya?,” Inji Musa Umar.

NAN

LEAVE A REPLY