Rundunar ‘yan sintiri dake Birnin Kebbi ta kama wani mutum dan shekara 30, wanda nakasasshe ne da laifin yiwa yara kanana guda hudu fyade a yankin Dabariya dake Birnin Kebbi a jihar Kebbi.

Alhaji Lawal Augie, shi ne Shugaban kungiyar ‘yan sintirin, ya shaidawa manema labarai a Birnin Kebbi ranar Alhamis.

Yace, mutanan  yankin ne suka kama mutumin a lokacin da yake aikata masha’a da kananan yaran.

“A ranar Laraba da daddare, mun samu kira daga uban kasar Badariya; inda yake shaida mana cewar, an kama wani musaki a yankin yana yiwa kananan yara guda hudu fyade”

“An ce yaran ‘yan talla ne a yankin”

“Daga nan muka tura zaratan matasanmu,inda ba da bata lokaci ba suka cukumo shi, suka kuma danka mana shi domin gudanar da bincike”

“Daga bisani mun tura al’amarin zuwa ga hukumar Hisba ta jiha domin daukan matakin da ya dace”

Malam Lawal Augie yace, mutumin ya taba aikata irin wannan laifi a yankin karamar hukumar Jega, da aka korshe ne ya dawo Badariya a yankin hukumar mulki ta Birnin Kebbi”

Daga nan ya bukaci iyaye da su sanya ido sosai akan inda yaransu suke zuwa,da kuma wadan da suke mu’amala da su.

Daya daga cikin yaran da aka yiwa fyaden ta bayyana abinda aka yi mata da cewa “A ranar farko da muka hadu da shi, tun a shekarar 2017 ne, a lokacin ina tallar cincin a yankin Badariya inda yake dab da gidansa”

“Daga zarar yaji muryata ina talla, zai kirani gidansa, daga nan zai rike hannuna yana shafani, ni kuma sai na dauke wuta”

“Daga yaga haka shi kuma sai ya dauke ni zuwa kan gadonsa, ya biya bukatarsa”

“Na sanar da iyayena abinda yake faruwa, har mahaifina yayi barazanar kai shi kotu”

“Jiya ma bayan ya ganni, ya jani zuwa dakainsa, yana ta yi min dadin baki har na bashi kaina, kafin daga bisani a kama shi”

Mutumin ya shaidawa ‘yan jarida cewar, ya biyewa shaidan ne yasa ya aikata wannan abu da kananan yara.

“Ni dan asalin karamar hukumar Jega ne,kuma ina harkar saye da sayarwa ne”

“Ina da mata daya da yara uku, biyu mata daya namiji”

“Wannan shi ne karon farko da na tsinci kaina a irin wannan al’amari, kuma ba komai bane illa sharrin shaidan” A cewar musakin.

A lokacin da yake tattaunawa da manema labarai, uban kasar Badariya, Alhaji Muhammad Abdullahi, ya zargi iyaye da sakaci ta yadda suke dorawa kanan yara talla maimakon su tura su makaranta.

“Hakan ba yana nuna wanda ya aikata musu wannan abu yayi daidai ba, amma kyale yara kanana irin wannan suna talla mai makon zuwa makaranta, sam bai dace ba, iyayen yara su kansu suna da hannu kan abinda ya faru” A cewar uban kasar Badariya.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, ya ruwaito cewar yaran suna tsakanin shekaru 12 zuwa 13.

NAN

LEAVE A REPLY