Rundunar ‘yan sanda ta ta kasa reshen jihar Kaduna, ta bayyana cewar zata yiwa dajin Rigasa dake jihar Kaduna kofar rago, domin farautar miyagun mutane batagari da suke tayar da zaune tsaye, kuma suka fake a cikin dajin.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewar, a kalla ‘yan sanda hudu ne suka rasa ransu a a cikin dajin na Rigasa ranar Asabar a jhar kaduna, inda ‘yan ta’addan da suka yi mafaka a cikin dajin suka halaka su.

‘Yan sandan sun bayyana sunayen mutanan da aka kashe a cikin dajin da Isfekta Benard Odibo da Insfekta Mamman Abubakar da Insfekta Haruna Ibrahim da Sajan Emmanuel Istifanus.

A cewar sanarwar da rundunar ‘yan sandan ta fitar ta bakin kakakinta DCP Jimoh Moshood a ranar Litinin a babban birnin tarayya Abuja, an yiwa ‘yan sandan kwanton bauna ne aka kashe su, a lokacin da suke dawowa yayin da suka farwa wasu masu garkuwa da mutane.

 

LEAVE A REPLY