Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, a ranar Juma’a, sun tarwatsa mabiya addinin Shah da suke cigaba da yin zanga zangar kiran sai an saki Shugabansu Ibrahim El-Zakzaky.

Haka kuma,rundunar ta ci nasarar cafke wani mai ikirarin Gwagwarmaya don cigaban al’umma mai suna Deji Adeyanju, wanda shi ne yake yiwa mabiya addinin Shiah da suke yin zanga zangar a babban birnin tarayya Abuja.

Deji Adeyanju ya kasance gaba gaba wajen taya mabiya Shiah yin wannan zanga zangar a dandalin nan na Unity Fountain dake unguwar Maitama a Abuja, inda suke yin zaman dirshan.

Wannan kamun da aka yiwa Deji Adeyanju dai yana zuwa ne bayan ‘yan kwanaki da wata kungiyardake fafutikar tallata Shugaba buhari ta nemi a kama shi, akan wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels, a cewar jaridar Punch.

‘Yan kungiyar dai sun yi ikirarin cewar shi (Deji Adeyanju) yayi kazafi ga Shugaban kasa, inda suka ce shi Dejin yayi ikirarin cewar an garzaya da Shugaba Buhari zuwa asibiti ne cikin gaggawa yayin da ya isa birnin Landan na kasar Burtaniya.

Sai dai har ya zuwa wannan lokaci kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Anjuguri Manzah, bai amsa waya ko sakon tes din da aka aika masa ba, kan zargin da ake musu na tsare Deji Adeyanju.

LEAVE A REPLY